Close Menu
HAJJ CHRONICLES
  • Home
  • Hajj News
  • Global
  • Health
  • Nahcon
  • Picture Gallery
  • Opinion
  • Videos
  • HAUSA
Facebook X (Twitter) Instagram
HAJJ CHRONICLES
  • Home
  • About Us
  • Privacy Policy
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram
SUBSCRIBE
  • Home
  • Hajj News

    975 Kwara Pilgrims Airlifted for 2025 Hajj

    May 15, 2025

    First Hajj Pilgrims Arrive by Sea at Jeddah Islamic Port

    May 15, 2025

    Nigerian Pilgrims Begin Second Phase of 2025 Hajj Journey – By Aminu Kabir Muhammad

    May 14, 2025

    Niger State’s First Batch of Pilgrims Set for Airlift to Saudi Arabia

    April 30, 2025

    Jigawa Governor Appoints Emir of Kazaure as Amirul Hajj for 2025

    April 29, 2025
  • Global

    flyadeal Aims To Serve 75,000 International Hajj Pilgrims In 2025

    January 23, 2025

    Reflections on the 4th Hajj Conference and Exhibition in Jeddah – By Muhammad Ahmad Musa

    January 21, 2025

    Hajj and Umrah Expo 2025: Innovation and Collaboration Take Center Stage in Jeddah – By Fatima Sanda Usara

    January 14, 2025

    Makkah Red Crescent Boosts Preparedness to Heavy Rainfall

    January 6, 2025

    Intense Rainfall Sweeps Through Makkah, Madina and Jeddah

    January 6, 2025
  • Health

    Gombe Muslim Pilgrim Board Commences Vaccination for 2025 Hajj Pilgrims – By Abdulqadir Aliyu Shehu

    April 28, 2025

    NAHCON Inaugurates Committee To Review National Medical Team Guidelines for Hajj 2025

    December 19, 2024

    Saudi Health Minister Strengthen Ties With Greece On Health Cooperation During Official Visit

    November 23, 2024

    Umm Al-Qura University volunteers extend help to pilgrims in Mina during Tashreeq

    June 17, 2024

    Hajj 2024: African pilgrim airlifted for emergency care

    June 14, 2024
  • Nahcon

    NAHCON Intensifies Efforts in Makkah to Fast-Track Nusuk Card Distribution for Nigerian Pilgrims

    May 22, 2025

    NAHCON Chairman Tasks Media Team on Fair, Responsible Coverage of 2025 Hajj

    May 20, 2025

    NAHCON Steps Up Oversight of Tour Operators’ Catering Ahead of 2025 Hajj

    May 19, 2025

    NAHCON Chairman Applauds Madinah Operations Team, Hails Stakeholder Collaboration

    May 18, 2025

    NAHCON Ensures Quality Feeding for Over 17,000 Nigerian Pilgrims in Madinah – By Ahmad Mu’azu

    May 16, 2025
  • Picture Gallery
  • Opinion

    Exposing Leadership Newspaper’s many lies against NAHCON chairman – By Ahmad Shafi’i PhD

    May 8, 2025

    What Do the Enemies of NAHCON Chairman Really Want? 

    May 3, 2025

    Who Will Now Thank the NAHCON Chairman? By Assalafy Yola

    April 29, 2025

    Hajj Commission, Professor Abdallahi Saleh, VP Shettima and the Daily Nigerian Report – By Uncle Anas Dukura

    April 18, 2025

    Who Is After the NAHCON Chairman? By Assalafy Yola

    April 9, 2025
  • Videos
  • HAUSA
HAJJ CHRONICLES
Home » Na Zo Hukumar NAHCON Ne Da Kyawawan Manufofi – Farfesa Abdullahi Sale
Nahcon

Na Zo Hukumar NAHCON Ne Da Kyawawan Manufofi – Farfesa Abdullahi Sale

adminBy adminDecember 12, 2024No Comments4 Mins Read
Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Email Telegram
Farfesa Abdullahi Sale
Farfesa Abdullahi Sale

Daga Shafi’i Sani Muhammad

A wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya jaddada aniyarsa na gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 cikin sauki da nasara. Ya bayar da wannan tabbacin ne a jawabinsa a taron da aka gudanar a hedikwatar hukumar NAHCON da ke Abuja.

 

Farfesa Saleh ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba da damar gudanar da taron tare da jaddada sadaukarwar Hukumar na shawo kan kalubale da kuma sake mayar da hankali don samun inganta aiki.

 

A cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana kalubale da dama da ya tarar lokacin da aka nada shi mukamin, da suka hada da ikrarin da ba a warware ba da kuma cikas wajen gudanar da ayyukan da suka kawo tasgaro ga ci gaban wasu muhimman ayyuka.

Ya kuma baiwa masu ruwa da tsaki tabbacin ci gaba da kokarin shawo kan wadannan matsalolin. “Alhamdulillah, a yau dukkanmu muna nan a matsayin abokan aiki, muna hada kawunanmu wuri guda domin magance kalubalen da ke gabanmu da kuma yin aiki a matsayin wata babbar kungiya domin tallafa wa daya daga cikin shika-shikan Musulunci,” inji shi.

 

Ya bayyana wasu daga cikin batutuwan da ake ta cece-kuce da su kawo yanzu, da suka hada da mayar da Riyal 150 na Saudiyya da rashin rashin da wutar lantarki ingantacciya a lokacin aikin Hajjin 2023.

 

Farfesa Saleh Usman ya tabbatar da cewa shugabancinsa na aiki tukuru don ganin an daidaita kudaden hidimar kashi 2% da aka warewa hukumar alhazai ta jiha dangane da aikin Hajjin 2024.

Shugaban ya kuma yi alkawarin biyan dukkanin wasu hakkoki da aka nema wadanda suka yi daidai da doka, tare da aza harsashin wani sabon babi na ayyukan NAHCON. Farfesa Saleh ya yi kira ga shugabannnin hukumomin alhazai na jahohi dasu gaggauta sanya kudade ga Hukumar domin samun damar yin shiri da wuri, da suka hada da samar da gidaje masu araha da dacewa a Madina, Makkah, Mina da Mashaer.

 

Ya kuma sanarwa da taron cewa zai fara ziyarce-ziyarce a shiyyoyin kasar nan guda shida domin tattaunawada malaman addini da sarakunan gargajiya domin samun goyon baya da albarkar aikin Hajjin 2025 da kuma ziyarar farko kafin aikin Hajji a kasar Saudiyya wanda zai gudana a watan Janairun 2025 wanda ya kunshi wakilai daga duka NAHCON da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi wadanda za su halarci tarukan shirye-shiryen aikin Hajji, tare da kammala yarjejeniya da hidimar alhazai, da kuma duba shirye-shirye a Jeddah.

 

Shugaban hukumar ta NAHCON ya kuma jaddada muhimmancin hada kai, inda ya bayyana ma’aikatan NAHCON da shuwagabanni/masu ruwa da tsaki na jahohi a matsayin manyan ginshikan hukumar.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsayin abokan aiki daya domin cimma manufa daya ta samar da aikin Hajji mai cike da inganci ga alhazan Najeriya.

 

A cikin kalamansa, “Na zo nan ne da kyakkyawar niyya da kuma tsare-tsare masu yawa na kawo sauyi  fasalin Hukumar.

Mu bude sabon shafi mu sanya Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jiha ta NAHCON ta zama abin koyi don jin dadin Alhazan Najeriya,” inji shi.

 

Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan aiyuka na hukumar,  Prince Anofi Olarewaju Elegushi ya bayar da bayanai kan kalandar Hajji ta 2025, inda ya bayyana cewa an raba takardar jagora mai shafuka 51 daga ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya don daidaita ayyukan.

An yi kira ga masu ruwa da tsaki da su fahimci ka’idojin da kuma bin ka’idojin aiki.

 

Taron ya kuma tabo batutuwan da ba a warware su ba daga aikin Hajjin 2024 inda Kwamishinan hukumar mai  Kula da Ma’aikata da Kudi (PPMF),  Aliu Abdulrazak ya bayyana cewa Shugaban Hukumar NAHCON ya ba da izinin fara biyan kudaden da Jihohi ke biya bayan an kammala sulhu da su da sashen Kudi da Asusu.

 

An kammala taron inda shugaban ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagora da nasara, tare da jaddada kudurinsa na hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin isar da sako mai inganci. Ya nanata muhimmancin hadin kai tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su rungumi zaman lafiya domin samun nasarar aikin Hajji na shekarar 2025 tare.

Farfesa Abdullahi Sale Hajj 2025 NAHCON
Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp

Related Posts

NAHCON Intensifies Efforts in Makkah to Fast-Track Nusuk Card Distribution for Nigerian Pilgrims

May 22, 2025

NAHCON Chairman Tasks Media Team on Fair, Responsible Coverage of 2025 Hajj

May 20, 2025

NAHCON Steps Up Oversight of Tour Operators’ Catering Ahead of 2025 Hajj

May 19, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

Don't Miss
Nahcon

NAHCON Intensifies Efforts in Makkah to Fast-Track Nusuk Card Distribution for Nigerian Pilgrims

By adminMay 22, 20250

With the Tashriq days fast approaching, the National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) has stepped…

NAHCON Chairman Tasks Media Team on Fair, Responsible Coverage of 2025 Hajj

May 20, 2025

NAHCON Steps Up Oversight of Tour Operators’ Catering Ahead of 2025 Hajj

May 19, 2025

Governor Inuwa Yahaya Bids Farewell to First Batch of Gombe Pilgrims for 2025 Hajj – By Abdulkadir Aliyu Shehu

May 19, 2025
Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • WhatsApp
Our Picks

NAHCON Intensifies Efforts in Makkah to Fast-Track Nusuk Card Distribution for Nigerian Pilgrims

May 22, 2025

NAHCON Chairman Tasks Media Team on Fair, Responsible Coverage of 2025 Hajj

May 20, 2025

NAHCON Steps Up Oversight of Tour Operators’ Catering Ahead of 2025 Hajj

May 19, 2025

Governor Inuwa Yahaya Bids Farewell to First Batch of Gombe Pilgrims for 2025 Hajj – By Abdulkadir Aliyu Shehu

May 19, 2025
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Home
  • About Us
  • Privacy Policy
  • Contact Us
© 2025HAJJ CHRONILES

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.