Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta lura da umarni na baya-bayan nan da kungiyar Kamfanonin masu gudanar da aikin Hajji da Umrah a Najeriya (AHOUN) ta bayar na umurtar wakilansu da su dakatar da shiga shirye-shiryen Hajjin 2025.
A yayin da muka amince da batutuwan da suka taso dangane da kudaden da aka tara, yana da kyau mu fayyace cewa NAHCON ta ci gaba da tattaunawa da AHOUN kan wannan al’amari kuma ta jajirce wajen magance duk wata matsala da ta dace. Jinkirin da aka samu wajen warware wasu batutuwan da suka shafi kudi ya samo asali ne daga sarkakiyar ayyukan Hajji, wadanda suka shafi masu ruwa da tsaki a cikin gida da waje, ciki har da hukumomin Saudiyya.
A sanarwar da mataimakiyar Daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, t ace NAHCON na son tabbatar wa AHOUN da sauran al’umma cewa Hukumar ba ta da niyyar ragewa ko yin watsi da batun mayar da kudaden. A ranar 24 ga Satumba, 2024, NAHCON ta yi magana da AHOUN game da gaggawar daidaita kalandar Hajjin Saudiyya don gujewa kawo cikas a shirye-shiryen Hajjin 2025, matsayin da muke da shi har yanzu.
A kwanannan ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ba da umarnin cewa manyan kamfanoni 20 ne kawai za su shirya aikin Hajji daga Najeriya domin samun saukin daidaitawa da kuma tsara yadda ya kamata. Sai dai kuma bisa gaskiya NAHCON ta amince da hadewa da hadin gwiwa domin bai wa duk masu sha’awar ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci amma da nufin yi wa alhazai hidima cikin gamsarwa.
Don haka a matsayinta na masu kula da kamfanonin, NAHCON ta yi imani da cewa bude tattaunawa da ci gaba da yin hadin gwiwa su ne mafi kyawun hanyoyin warware wadannan al’amura ba tare da haifar da tarzoma da ka iya shafar alhazai da masu gudanar da aikin ba. Hukumar NAHCON ta ci gaba da tattaunawa da AHOUN domin kawar da duk wata damuwa da ke daurewa da kuma kokarin ganin an cimma matsaya cikin gaggawa.
A halin da ake ciki, NAHCON ta shawarci shugabannin AHOUN da mambobinta da su bar shirye-shiryen da ake yi ya samar da sakamakon da ake bukata ba tare da kawo cikas ga shirin gudanar da ayyukan Hajji na 2025 kan lokaci ba. Wannan shi ne mafi alheri ga dukkan bangarorin da abin ya shafa domin tare da ko babu AHUON, Arafat zai ci gaba da rike ranar da aka kayyade.
Kofar NAHCON a bude take domin tattaunawa.