A halin yanzu hukumar alhazai ta kasa NAHCON na gudanar da taro da Sakatarorin Zartarwa na hukumomin alhazai na jihohi a dakin taro na NAHCON a yau 23 ga watan Satumba.

Taron da ke gudana tsakanin Hukumar NAHCON da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha na gudana ne karkashin jagorancin Kwamishinan Ayyuka, Prince Enofi Elegushi.

A cewar sashin yada labarai na hukumar, taron na shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2025 ne kuma a halin yanzu yana gudana ne a babban dakin taro na Hukumar dake Abuja.


