Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) tare da shugabancin kungiyar shugabannin hukumomin alhazai na Jihohi a fadin Najeriya, karkashin jagorancin Malam Shitu na NAHCON da Alhaji Abubakar Salihu (Jihar Adamawa), sun mika sakon jaje ga Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi sakamakon wata gobara da ta auku a gidansa kwanan nan.
A sanarwar da Musa Bello na tawagar yan jaridun kan aikin haji na Kebbi ya fitar, yace Haka kuma, kungiyar ta jajanta wa Gwamnatin Jihar kan rasuwar Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar, marigayi Hon. Muhammad Usman Ankwe.
Kungiyar, wanda ta kunshi shugabanni da manyan jami’an hukumomin jin dadin alhazai daga jihohi daban-daban, ta bayyana matukar damuwa kan wannan lamari, tare da yi wa Shugaban Kebbi da iyalansa addu’ar samun juriya da karfin gwiwa a wannan lokaci mai cike da jarrabawa.
A sakonni daban-daban da aka aike wa Shugaban, mambobin kungiyar sun bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai radadi, suna mai cewa irin wadannan masifu na bazata na tunatar da bukatar hadin kai da taimakon juna a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da aikin Hajji.
Sun kuma yabawa Shugaban, Alhaji Faruku Aliyu Yaro, bisa jajircewarsa da gudummawar da yake bayarwa wajen tabbatar da ingantaccen tafiyar da harkokin Hajji a Najeriya, tare da karfafa masa gwiwa da ya ci gaba da jajircewa duk da wannan kalubale.
A nasa bangaren, Alhaji Faruku Aliyu Yaro ya gode wa Hukumar NAHCON karkashin jagorancin Ambasada Abba Ismail, wanda Daraktan Gudanarwa na Hukumar ya wakilta, tare da Sakataren Zartarwa na Jihar Adamawa da tawagarsu bisa ziyarar jaje da suka kai masa, inda ya yi musu addu’ar dawowa gida lafiya.
Haka zalika, sauran masu ruwa da tsaki a bangaren Hajji da jami’an gwamnati sun aike da sakonnin ta’aziyya, tare da yi masa addu’ar samun saukin wannan rashi da ya fuskanta.
Musa Bello
Kungiyar Yada Labarai ta Alhazai ta Jihar Kebbi
Juma’a, 10 ga Afrilu, 2026

