Daga Shafii Sani Mohammed da Abdulbasit Abba A ci gaba da ganawar sabunta fahimta da masu ruwa da tsaki a harkar Hajji, Hukumar Alhazai ta Kasa, (NAHCON), ta kara fayyace batutuwan da suka shafi daidaita kujerun Hajjin 2026, sharuddan binciken lafiya, tsarin bayar da biza, da kuma manyan sauye-sauyen aiki bayan taron tuntuba da Kamfanonin Jirgin yawo masu lasisi.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Hukumar, Ambasada Ismail Yusuf Abba, ya jaddada cewa NAHCON hukuma ce ta tsari da sa ido wadda aka kafa domin bayar da lasisi, kula da bin ka’ida da tabbatar da gaskiya a harkokin Hajji da Umrah.
Ya bayyana cewa Hukumar za ta kara tsaurara hanyoyin sa ido kan ayyuka tare da daukar matakin ladabtarwa ga duk wanda ya karya doka, ciki har da dakatarwa ko janye lasisi idan ya zama dole.
Hukumar ta sake nanata cewa sauyin da aka samu a karin kujerun Hajji ya samo asali ne daga matakin rabon kujeru na duniya da hukumomin Hajji na Saudiyya suka yanke, ba mataki ne da NAHCON ta dauka ita kadai ba.
Rabon kujerun kasa yana karkashin ikon Masarautar Saudiyya ne bisa la’akari da karfin aiki da kuma tsaro.
Dangane da batun kujerun Najeriya, an bayyana a taron cewa NAHCON ba ta da ikon kara ko rage adadin da aka amince da shi. Don haka, Hukumar ta bukaci masu ruwa da tsaki da jama’a su yi watsi da duk wata jita-jita da ke nuna cewa akwai son kai ko nuna wariya wajen rabon kujeru.
Adadin kujerun da aka amince wa Najeriya yana nan daram, kuma an raba cikin adalci bisa tsarin da aka tanada.
Kamfanonin Jirgin yawo da suka nuna damuwa kan asarar kudi sakamakon yarjejeniyoyin da suka riga suka kulla, an bukace su da su gabatar da korafinsu a rubuce tare da hujjoji domin duba su. Hukumar ta tabbatar da cewa za a tantance duk wata sahihiyar kara bisa tsarin doka da hanyoyin diflomasiyya idan ya dace.
Shugaban Tawagar Lafiya ta NAHCON, Dakta Ibrahim Abubakar, ya bayyana cewa takardar shaidar binciken lafiya wajibi ne kuma tana da alaka kai tsaye da bayar da biza.
Domin tabbatar da inganci da dakile magudi, NAHCON ta takaita bayar da takardar shaidar lafiya ga manyan asibitocin gwamnati masu inganci. Dole ne kowace takardar ta kunshi cikakken bayanin likita, ciki har da rajista a Majalisar Likitoci da Hakoran Najeriya (MDCN), domin tabbatar da sahihanci.
Hukumar ta kara bayyana cewa:
Wannan mataki an dauke shi ne domin hana jabun takardun lafiya da magudi.
Jihohi da dama sun riga sun fara bin ka’idar binciken lafiya yadda ya kamata Sharadin ya yi daidai da jadawalin bayar da biza na Saudiyya.
NAHCON ta gargadi cewa duk wanda ya gabatar da bayanan lafiya marasa inganci ko na karya zai fuskanci hukunci mai tsanani. Duk da matsin lokaci, Hukumar ta ce dole ne a gaggauta domin kauce wa jinkirin biza.
Game da tsarin bayar da biza, NAHCON ta bayyana cewa ta gaji tsarin da ake amfani da shi, sannan ta sake duba shi bisa la’akari da kalubalen da aka fuskanta a baya, ciki har da batun ɓacewar wasu mahajjata.
Hukumar ta kuma bayyana cewa kokarin yin gyare-gyare ya fuskanci turjiya daga wasu bangarori da ke cin moriya daga tsarin da ba ya da gaskiya. Sai dai ta jaddada kudirinta na samar da tsari mai tsafta, mai sauki da kuma adalci wanda zai amfani kowa baki daya.
NAHCON ta bukaci hadin kai, gaskiya da rikon amana daga dukkan masu ruwa da tsaki, tare da gargadin cewa duk wani mataki da zai kawo cikas ga kokarin gyara tsarin ba za a lamunta da shi ba.
Hukumar ta sake tabbatar da cewa:
Kamfanonin da suka yi aiki nagari za a yaba musu kuma a karfafesu.
Duk wani karya ka’ida zai jawo hukunci daidai da laifi.
Bin doka da kwarewa su ne ginshikin aiki.
Shugaban Hukumar ya kuma umurci Sashen Yada Labarai na NAHCON da ya kara himma wajen isar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin kawar da rudani ga mahajjata da masu kamfanoni.
Dangane da harkokin Umrah, yarjejeniyar masu ba da hidima da matsalolin kudi da aka gabatar, NAHCON ta sanar da cewa za ta kira babban taron tuntuba bayan kammala Hajji domin samar da matsaya mai dorewa da gyare-gyare na dindindin.
A halin yanzu, Hukumar ta ce babban burinta shi ne tabbatar da nasarar gudanar da Hajjin 2026 cikin tsari, sauki da inganci domin amfanin alhazan Najeriya.
NAHCON ta jaddada aniyarta na:
Bayar da sahihan bayanai cikin gaskiya
Raba kujeru cikin adalci
Tsaurara sa ido da aiwatar da doka
Ci gaba da tuntuba da Kamfanonin Jirgin yawo masu lasisi
An shawarci masu ruwa da tsaki da jama’a da su dogara kacokan da sanarwar hukuma ta NAHCON domin samun sahihan bayanai.

