Daga Muhammad Ahmad Musa, tare da karin rahoto daga Suwaiba Ahmad da Mariam Zubair Abubakar
A yayin da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2025 suke kara zurfafa, Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya jagoranci wata tawaga domin duba yadda kamfanonin da aka bai wa kwangilar yiwa Alhazan Najeriya HIDIMA suke shirye-shiryen gudanar da ayyukansu a lokacin ibadar Hajj.
Gaskiyar Lamari Tsakanin Hukumar NAHCON da Kamfanin Mashariq Al-Dhahabiah – NHMST
Yayin ziyarar tawagar shugaban NAHCON zuwa ofishin kamfanin Mashariq Aldhahabiah, mai kula Masu Kula da Masha’ir, Farfesa Saleh ya jaddada kudirin hukumar na ganin komai ya tafi yadda ya kamata. “Biyo bayan ziyararku zuwa Najeriya kwanan nan, yana da muhimmanci mu ci gaba da samun bayanai kan shirye-shiryen ku da kuma kalubalen da za su iya tasowa. Babban manufarmu shi ne tabbatar da kowanne Alhajin Najeriya ya samu ingantacciyar kulawa da hidima mai kyau daga farko zuwa karshen ibadarsa,” inji shi.
Shugaban Mashariq Aldhahabiah, Muhammad Amin Bin Hassan Andergiri, ya yaba wa hukumar kan jajircewarta. “Kamfaninmu yana nan cikin shiri domin tabbatar da samar da ingantattun ayyuka. Mun shirya ziyarar Gani da ido domin nuna muku irin shirinmu da tabbatar muku da cewa muna cikin cikakken shiri,” Andergiri ya bayyana.
Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Prince Anofi’u Olanrewaju Elegusi, ya jaddada muhimmancin bayyana shiryen shiryen a fili, yana mai cewa, “NAHCON dole ta kasance tana da cikakken bayani kan kowanne mataki na kwangilolin ayyukan da aka bayar. Ina kira gare ku da ku tabbatar da tsaftatattun wurare da kuma kula da jin dadin Alhazai bisa kololuwar ka’idoji.”
Tawagar ta ziyarci kamfanin Ekram Aldyf, inda Farfesa Saleh ya sake jaddada bukatar ingattatun ayyuka. “Nasarorin hukumomin Saudiyya wajen kulawa da jin dadin Alhazai ya samo asali ne daga sadaukarwa ga jin dadin bakin Allah. Kasancewarmu a nan wata shaida ce ta jajircewarmu wajen ganin an samu hadin gwiwa dan fuskantar kowanne irin kalubale fa ka Iya tasowa domin Alhazan Najeriya su samu ingantacciyar kulawa wajen ibada,” ya bayyana
Shugabannin Ekram Aldyf sun tabbatar wa NAHCON cikakken shirinsu, tare da gabatar da ma’aikatan da aka tanada da kuma kayayyakin da aka ware domin Alhazan Najeriya yayin zamansu a wuraren ibada.
NAHCON ta sake tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kula da jin dadin Alhazai, tare da aiki kafada-da-kafada da kamfanonin domin ganin aikin Hajjin 2025 ya gudana cikin sauki da jin dadi ga mahajjata Najeriya.