Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kara karfafa tsarin Ajiya na Hajj (Hajj Savings Scheme HSS) ta hanyar rattaba hannu kan Yarjejeniyar Aiki (MoU) da manyan bankuna hudu na musamman Alternative Bank, Jaiz Bank, Lotus Bank da TAJ Bank.
A wata sanarwa da Mataimakiyar Darakta a Sashen Labarai da Hulda da Jama’a ta Hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa kowanne daga cikin bankunan zai samar da ingantaccen dandalin rajistar alhazai ta yanar gizo da kuma tafiyar da kudaden HSS bisa ka’idojin tsarin kudi na Islama. Bankunan za su kuma gabatar da cikakken taswirar aiwatarwa domin tabbatar da gaskiya, kare amana, da kuma fadada damar shiga tsarin a fadin kasar.
Yayin taron rattaba hannun, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana shirin Hajj Saving Scheme a matsayin wata hanya tsari ce da za ta bai wa ’yan Najeriya damar shirin Hajj tun da wuri. Ya ce akwai masu sha’awar shiga tsarin da dama, sai dai rashin isasshen wayar da kai na hana wasu fahimtar amfaninsa. Ya tabbatar da cewa NAHCON tare da bankunan za su kara kaimi wajen fadakarwa ta hannun malamai, kafafen gargajiya da na zamani, domin kara fahimtar jama’a game da fa’idodin dogon lokaci na tsarin. Ya yabawa sashen HSS da bankunan bisa jajircewarsu.
Kwamishinan Tsare-tsare, Ma’aikata, Gudanarwa da Kudi (PPMF), Prince Abdulrazaq Aliu, ya taya bankunan murnar wannan zabe, inda ya ce an zaɓe su ne bisa kwarewa da cancantarsu. Ya jaddada bukatar samar da tsarin kimanta aikin bankunan lokaci–lokaci domin tantance ci gaban shirin. Ya tabbatar da cewa NAHCON za ta samar da sahihin dandamali, ka’idoji da kulawar da ake bukata domin nasarar HSS.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka, Prince Anofiu Elegushi, ya bayyana HSS a matsayin tsarin rayuwa ga gudanar da Hajjin nan gaba, musamman duba da hangen nesa na Saudiyya na Vision 2030. Ya ce ba zai yiwu Najeriya ta ci gaba da dogaro da tsohon tsarin shirya Hajj ba sannan ta yi tsammanin kasashen Saudiyya za su yi da ita kafada da kafada. Ya tabbatar da cewa HSS zai samar da kundin sunayen alhazai tun da wuri domin kowanne lokaci da ake bukatar bayanai.
A jawabin rufewa, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Bayanai da ayyukan na Laburare (PRSILS), Farfesa Abubakar Yagawal, ya nuna farin cikinsa tare da bayyana cewa wannan sabuwar karfafawa da aka yi wa HSS ya kusan warware matsalar Hajj ta Najeriya da kashi 99.9%. Ya yi hasashen cewa ba da jimawa ba Najeriya za ta kai matsayin kasashen dake da ingantaccen tsarin Hajj kamar Indonesia.
Da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna din, bankunan an amince da su a hukumance su fara amfani da dandalansu na intanet wajen rajistar masu niyyar zuwa Hajj tare da zuba jarin kudaden alhazai cikin halal–halal kadai. A baya NAHCON ta riga ta tantance tsarin dandalan da kowanne banki ya gabatar.
Hadin gwiwar ta kunshi wakilai kamar su: Malam Garba Mohammed da Mohammed Abdul daga The Alternative Bank; Dr. Haruna Musa Managin Director, da Alhassan Abdulkareem daga Jaiz Bank; Akin Adekoke daga Lotus Bank; da Alhaji Hameed Joda –Managin Director, daga TAJ Bank.
Da yake jawabi a madadin bankunan, Dr. Haruna Musa ya gode wa NAHCON tare da tabbatar da cikakken goyon bayan bankunan ga nasarar shirin. Ya ce za su yi amfani da fasahar zamani tare da kafofin gargajiya wajen wayar da kai. Ya kara da cewa da zarar HSS ya cimma nasara, gudanar da Hajj a Najeriya zai shiga sabon matsayi na inganci.

