Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, na sanar da dukkan masu ruwa da tsaki, alhazai da kuma jama’a cewa Hukumar ta kammala shirye-shiryen masaukin alhazai na Hajjin 2026 a biranen Makkah da Madinah, tun kafin cikar wa’adin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Kammala shigar da bayanan masauki da kuma amincewa da su daga Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ya zo ne bisa umarnin Mataimakin Shugaban Ƙasa na Tarayyar Najeriya, Mai Girma Kashim Shettima, GCON, wanda ya jaddada cewa dole ne a kammala muhimman shirye-shiryen aikin Hajji cikin wa’adin da Saudiyya ta amince da shi, domin kare muradun Najeriya a bangaren gudanarwa.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana godiyarsa ga Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa jagoranci da goyon bayan da ya bayar a duk tsawon wannan aiki, tare da yaba rawar da tawagar manyan jami’ai da aka tura Saudiyya, wadanda suka hada da yan Hukumar Gudanarwar NAHCON, tawagar Nusuk Masar, shugabancin kungiyar Shugabannin Hukumomin Alhazai na Jihohi, ma’aikatan NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki suka taka rawa wajen kammala shirye-shiryen samar da masaukin.
Da kammala wannan tsari, Najeriya ta tabbatar da masaukin alhazanta na Hajjin 2026, tare da kasancewa cikin ƙasashen da suka cika wannan muhimmin sharadi a cikin wa’adin da aka kayyade.
Yanzu haka Hukumar ta shiga mataki na gaba na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2026.

