Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta umurci dukkan kamfanonin daukar mahajjata na 2026 tare da hadin gwiwar Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su fara fitar da tikitin jirgi ga dukkan mahajjatan da za su tashi domin gudanar da ibadar Hajj ta 2026.
A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar yada labarai da hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara ta sanayawa hannu, tace wannan umarni ya fito ne yau 4 ga Disamba 2026, a wani taro da NAHCON ta gudanar tare da hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin jiragen 2026 a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Umarnin na nufin tabbatar da cewa kowane mahajjaci ya san takamaiman jadawalin tashinsa wanda ya hada da kwanan wata, lokaci da filin jirgin da zai tashi. Hakan zai taimaka wajen rage matsalolin kuskuren bayanan kafin saukar alhazai da ake turawa Saudiyya, wanda ke janyo tsaiko wajen rabon katin Nusuk da sauran shirye-shiryen aiki.
A fara Hajj na 2026, duk mahajjacin da ya rasa jirgi zai fuskanci hukunci mai tsanani. Wannan saboda an haɗa tikitin kowane mahajjaci kai tsaye da katin Nusuk, wanda za a ajiye shi a cikin motocin da aka ware musu a Saudiyya, wadanda za su kaisu otel dinsu.
Saboda haka, bayan fitowar visa, ba zai kara yiwuwa ga mahajjaci ya canza rukuni ba; za su zauna cikin kungiyoyin da aka samar da musu visa. Kowace rukuni na mutum 45 za su tafi tare, su zauna tare a Makkah, Madinah da Masha’ir, sannan su dawo tare zuwa Najeriya bayan kammala Hajj.
Haka kuma, dole ne NAHCON ta shigar da bayanan kafin saukar alhazai a dandalin Nusuk Masar awanni 72 kafin tashin kowanne jirgi. Bayanannin sun hada da lambar rukuni, sunayen alhazan rukuni, bayanan masauki, ginin da aka ware, da lambar gadon kwana. Duk mahajjacin da bai bayyana a filin jirgi ba a lokacin da aka tsara, za a dauke shi a matsayin wanda bai zo ba kuma zai biya tarar da ta shafi kujerar da bai yi amfani da ita ba. Wannan hukunci zai shafi duk wani bangare da ya yi sakaci.
Haka nan, Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya ta gabatar da sabon katin shiga jirgi da za a raba wa kowane mahajjaci kafin tashi. Katin zai ƙunshi muhimman bayanai irin su: sunan kamfanin jirgi, yawan kujeru, sunan jiha, sunayen mahajjata a cikin jirgin, filin tashin jirgi, lokaci, filin sauka da lokacin zuwan jirgi.
Mai taimakawa shugaban NAHCON kan al’amura na musammam, Dr. Danbaba Haruna, ya bayyana cewa hukumar ta kammala yin ajiyar sansani da sauran ayyuka. Sai dai idan adadin ajiyar bai dace da aikin masauki da Saudiyya ta tanada ba, za a mayar da kudaden da suka wuce a asusun NAHCON, kuma hakan na nufin an rasa guraben. Ya ja hankalin Hukumar Alhazai ta Jihohi da su gaggauta tura kudaden Hajj domin kauce wa rasa karin gurabe.
NAHCON ta kara jaddada cewa sabon sharadin lafiya da Saudiyya ta kafa dole ne a bi shi sosai domin akwai hukunci ga masu karya doka.
Ma’aikatar Hajj da Umrah ta ce duk mahajjacin da aka samu da daya daga cikin cututtukan da ke hana tafiya, ba zai yi Hajj ba, kuma zai biya kudin korarsa idan ya tafi. An umurci hukumomin alhazai na jihohi da su yi aiki ne kawai da cibiyoyin lafiya masu inganci da aka tantance wajen bayar da takardar shaidar lafiya. Cutar da ke hana zuwa Hajj sun hada da: gazawar manyan sassan jiki (zuciya, hanta, koda, da huhu), marasa lafiya masu karbar chemotherapy ko radiotherapy, cututtukan hauka ko lalacewar kwakwalwa da ke rage natsuwa, mantuwa mai tsanani, ciki mai hadari a kowane mataki, da cututtuka masu yaduwa.
A wani bangare, an riga an aika rabon jiragen 2026 ga kowace Hukumar Alhazai ta Jihar tare da shawarar su yi hadin gwiwa. Sai dai rabon na iya canzawa saboda binciken fasaha da na kayan aiki. Kamfanonin jirgin 2026 sune: Air Peace, FlyNas, Max Air da Umza Air.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin hukumomin alhazai na jihohi, kamfanonin jirgi da hukumar NAHCON, yana mai cewa nasarar NAHCON nasarar kowa ce.

