Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta jinjinawa Hukumar Jin Dadin Mahajjata ta Jihar Kano kan jajircewarta da kuma kyakkyawan aiki wajen shirye-shiryen gudanar da Hajj na 2026.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace yayin wani taron hadin gwiwa da aka gudanar tare da dukkan Hukumomin Jin Dadin Alhazai ta jihohi a yau a Abuja
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana cewa hukumar ta riga ta tura fiye da naira biliyan 22 zuwa ga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON).
Ya ce wannan adadin kudin da aka tura ya nuna irin jajircewar jihar Kano wajen tabbatar da sahihin tsari, ingantaccen shiri da kuma kula lokaci wajen gudanar da aikin Hajj ga mahajjatan da ke shirin tafiya.
A nasa jawabin, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yabawa jihar Kano saboda kafa misali mai kyau a tsakanin sauran jihohi. Ya bayyana Kano a matsayin “jihar da ta bambanta da sauran jihohi”, yana jaddada gaskiya, inganci da kuma tsare-tsaren da aka yi cikin shiri tun da wuri.
Farfesa Usman ya kara yabawa jagorancin Hukumar kula da Jin Dadin ta Kano bisa ci gaba da inganta ayyukan hidima, kula da jin dadin mahajjata da kuma karfafa hadin kai tsakaninsu da hukumar NAHCON.
Shirye-shiryen da Jihar Kano ta yi tun da wuri da kuma cikakken biyan kudade sun sake tabbatar da aniyar jihar wajen tabbatar da cewa mahajjata masu niyyar zuwa Hajj za su samu kulawa, jagoranci da goyon baya mafi inganci a ziyarar su ta 2026.

