Tun bayan da aka nada Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) kuma babban jami’in hukumar alhazai ta kasa NAHCON, wasu mutane wadanda suka boye fuskarsu, suka fara yada labarai na karya da kuma kai hare-hare a kafafen yada labarai wadanda kawai manufarsu ita ce bata sunan babban malamin addinin musulunci da kuma kawo cikas ga ci gaban aikin Hajji a Najeriya.
Domin Kare Mutunci Da Martarbar Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman
Wadannan makiyan kawo gyara ba kawai adawa da mutumin da suke yi ba a kaikaice suna yaki ne da daya daga cikin manyan rukunan addinin musuluci wanda musulmin Najeriya suka dogara da yin aikin Hajji na gaskiya, inganci da araha ta hanyarsa.
Hajji ba shirin gwamnati ba ne kawai, yana daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.Don haka, dole ne a yi tambaya: Menene ribarsu ta hanyar yin zagon kasa ga irin wannan wajibi mai tsarki?
Dalilin Da Ya Sa Suke Shirya wannan makirci
Lamarin a bayyane yake cewa manufar wadannan masu cin zarafi ya samo asali ne daga son rai, adawar siyasa, da fargabar samun sauyi.
Tun hawansa shugabanci, Farfesa Abdullahi Saleh ya bullo da sauye-sauye na zamani, ya kawar da matsala da aka dade ana fama da ita, da kuma bijirewa tasirin da bai dace ba wajen zabar ma’aikata, matakin da ya kawo cikas ga wasu mutane da kungiyoyi da suka amfana da tsohon tsarin da ya lalace.
Tashin hankali na baya-bayan nan na gefe guda, rahotannin da ba a tabbatar da su ba, gami da labarin bata-gari kan zaben tawagar Hajjin 2025, misali ne na babba kan yadda suka zautu.Wadannan rahotanni ba a samo su ba ne don nuna damuwa ga jin dadin alhazan Najeriya;sun kasance sakamakon bacin rai daga waɗanda aka toshe musu gata ta haramtacciyar hanya.
Makirci Da Suka Shirya A Wajen Najeriya
Akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba amma masu tayar da hankali da ke nuni da cewa wadannan da ake kira musulmi da suka fake da sunan addini amma suna aikata abin da bai dace ba, sun tsara dabaru da dama don kawo cikas ga nasarar aikin Hajji ba kawai a Najeriya ba, har ma idan an je kasa mai tsarki.Ana zargin sun yi ganawar sirri da wasu kamfanonin yawon bude ido, kamfanonin jiragen sama, masu yi wa alhazai hidima, da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji domin dakile kokarin hukumar.
Shin sun yi imani da gaske cewa Allah zai ƙyale irin waɗannan munanan tsare-tsaren su yi nasara? Insha Allahu duk makirce-makircen da suke yi wa Musulunci da aikin Hajji mai alfarma zai lalace.
Ga wadanda suka kulla makirci don cutar da wannan al’amari mai daraja, Allah Ya juyar da makircinsu a kansu
Tambaya Kan Nagarta Da Munafunci
Wani abin ban mamaki shi ne, galibin kafafen yada labarai da ake amfani da su wajen tallata wadannan hikayoyin, mallakar Musulmi ne ko kuma ke tafiyar da su.
Wannan ya haifar da wata tambaya mai raɗaɗi: Shin da gaske waɗannan kafafe suna ɗaukan darajojin Musulunci da aikin jarida na ɗabi’a ne, ko kuwa sun zama kayan neman kuɗi da yin amfani da siyasa? Abin baƙin ciki ne cewa a lokacin da ya kamata mu goyi bayan mai gyara da gaske a wani muhimmin aiki na addini, wasu sun zaɓi su yi masa tawaye ta yin amfani da ƙagaggun labaran ƙarya da yada abubuwan raba hankalin jama’a.
Farfesa Saleh ba shi ne hukumar NAHCON ba, shidai kawai mai hidimtawa Al’ummah ne ya jajirce wajen dawo da martabar tsarin.Amincinsa ya ta’allaka ne ga alhazai, ba tare da wata maslaha ba.
Gyaran Da Yake Kan Aiwatarwa
Farfesa Abdullahi Saleh ya ci gaba da mai da hankali kan manufarsa ta neman agajin Ubangiji don gyara masana’antar Hajji da kuma sanya Najeriya a matsayin abin koyi a harkokin aikin Hajji a duniya.Yunkurin nasa ya riga ya fara samun karbuwa daga mahukuntan Saudiyya da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, sakamakon nuna gaskiya da tawali’u da kuma tsantsar fahimtar bangarorin aikin Hajji da na ibada.
Da yardar Allah da addu’ar ’yan Najeriya na gari, wadannan makiyan ci gaba ba za su yi nasara ba.Farfesa Saleh insha Allahu zai kammala wa’adinsa kuma mai yiyuwa ne ya ci gaba da aiki idan Allah ya so kuma shugabanni suka ga ya dace.
Aikin Hajji ba wai siyasa ko mulki ba ne. Ya shafi Imani da hadin kai da hidimtawa al’ummah. Kada mu ƙyale kanmu mu zama ‘yan amshin shata a hannun waɗanda suke neman raba mu da yin zagon ƙasa ga wannan babbar ibada.