Daga Abubakar Idi Maru, Abuja Shirye-shiryen aikin Hajjin 2026 na Nijeriya na fuskantar babbar barazana, sakamakon ƙara taɓarɓarewar dangantaka tsakanin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Masarautar Saudiyya (GACA).
Rahotanni na nuni da cewa hukumomin sufurin jiragen saman Saudiyya na tunanin ɗaukar matakan hukunci, ciki har da yiwuwar hana jiragen Nijeriya samun izinin sauka, bisa zargin cewa Nijeriya ta kasa bin ka’idojin Yarjejeniyar Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasashe Biyu (BASA) da aka cimma a 2015.
A cikin rikicin akwai gazawar NAHCON wajen tura cikakken jadawalin tashin jiragen Hajji ga GACA, wanda yake zama wajibi kafin a ba da izinin sauka da wucewa ta sararin samaniya a lokacin aikin Hajji.
Masana harkar jiragen sama na gargaɗin cewa ci gaba da jinkirta aika wannan jadawali na iya jefa Nijeriya cikin matakin hukunci daga Saudiyya, tare da haifar da babbar matsala ga dukkan tsarin jigilar alhazai.
Bincike ya nuna cewa rabon jihohi da jiragen sama da NAHCON ta fitar a watan Disambar 2025 bai yi la’akari da ragin yawan alhazai daga jihohin da aka bai wa kamfanin jirgin Saudiyya Flynas ba, yayin da aka ƙara wa jiragen Nijeriya kaso mai yawa. Maimakon a daidaita adadin domin cika sharadin rabon kashi 50–50 na BASA tare da fitar da jadawalin jirage mai inganci, ana zargin Hukumar ta bar wannan rashin daidaito ya ci gaba, lamarin da ya ƙara rikitar da tsarin shirye-shiryen GACA.
Wasu manyan majiyoyi a cikin NAHCON na zargin cewa lamarin ya wuce sakaci ko rashin ƙwarewa, suna danganta shi da ganganci da mugun nufi daga Kwamishinan Ayyuka na Hukumar, Prince Anofiu Elegushi. A cewar waɗannan majiyoyi, an yi watsi da matakan gyara da gangan duk da sanin cewa rashin amincewar jadawalin jirage na iya bai wa hukumomin Saudiyya damar takaita ko ma dakatar da jigilar alhazan Nijeriya, abin da zai cutar da walwalar alhazai da martabar Gwamnatin Tarayya a idon duniya.
Rikicin ya ƙara tsananta ne da ikirarin cewa wani tsohon mataimaki mai ritaya na ci gaba da tsoma baki a harkokin jiragen sama ba tare da wata doka ko izini ba.
Masana harkar sufurin jiragen sama na gargaɗin cewa wannan haɗakar tsoma bakin ciki, tangardar tsarin gudanarwa da rashin bin ƙa’idoji na iya sake tayar da rikicin da aka warware tun 2015, inda suka tunatar da cewa Nijeriya na cikin ƙasashe kaɗan da Saudiyya ta bai wa sassauci wajen aiwatar da BASA a hankali wata dama da ba a bai wa ƙasashe da dama masu aikin Hajji ba.
Da yake rahotanni ke nuna cewa hukumomin Saudiyya sun fara gajiya, masu ruwa da tsaki na jaddada cewa duk wani matakin hukunci da za a ɗauka zai fi shafar alhazan Nijeriya ta fuskar jinkirin jirage, rage kujeru ko ma hana shiga filayen jiragen saman Saudiyya a lokacin kololuwar aikin Hajji.
A sakamakon haka, ana kira da a gaggauta sa bakin Gwamnatin Tarayya, a hanzarta tura jadawalin jiragen Hajji da ya dace da BASA zuwa GACA, tare da gudanar da bincike a bayyane kan zargin ganganci na ciki, domin kauce wa rikicin da ka iya zama babbar matsala ta ƙasa, ta diflomasiyya da ta jinƙai.
Abubakar Idi Maru,
Ɗan jarida mai bincike,
Abuja.

