Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Ƙasar Saudiyya ta ƙara wa’adin cike bayanan alhazai da kuma tsara rukunan alhazai domin Hajjin shekarar 2026.
A sanarwar da mataimakiyar Daraktar yada da hulda da Jama’a ta Hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, tace bisa umarnin Mataimakin Shugaban Ƙasa na Tarayyar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tugga, ya tuntuɓi hukumomin Saudiyya domin neman ƙarin lokaci na musamman ga Najeriya don kammala cike bayanan alhazai. Hukumomin Saudiyya sun amince da wannan buƙata cikin karamci.
Sai dai ana sa ran cewa bayan ƙarewar wannan ƙarin lokaci, hukumomin Saudiyya ba za su sake amincewa da wani ƙarin lokaci ba, tare da jaddada muhimmancin gaggauta kammala aikin.
Don haka, an shawarci masu kula da harkokin Hajji da su yi aiki dare da rana domin tabbatar da kammala wannan aiki cikin gaggawa.
Wannan ƙarin lokaci ya zo ne ƙasa da awanni 48 bayan rufe dandalin Nusuk Masar na cike bayanai a duniya baki ɗaya.
Cikin sanarwar, an buƙaci hukumomin Hajji da su “kammala dukkan bayanan alhazai da ake buƙata cikin gaggawa domin kauce wa matsaloli a minti na ƙarshe.”
A wani labarin kuma, tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima bisa damar da aka ba shi na jagorantar NAHCON.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, 10 ga Fabrairu, 2026, inda ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya fara aiki daga Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.
An miƙa takardar murabus ɗin a rubuce ga Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa tanadin Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta 2006.
Farfesa Usman ya bayyana cewa dalilai na kashin kai, bayan nazari da addu’a, su ne suka sa ya yi murabus.
Ya kuma jaddada cewa murabus ɗin ba shi da alaƙa da rashin gamsuwa da Hukumar, Gwamnatin Tarayya, ko aikin NAHCON.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya karɓi ragamar shugabancin NAHCON daga Malam Jalal Arabi a ranar 20 ga Agusta, 2024, a matsayin mukaddashi, kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi a matsayin cikakken Shugaban Hukumar a ranar 10 ga Oktoba, 2024.
Yana da digirin farko daga Jami’ar Madina, digirin digirgir a fannin Nazarin Addinin Musulunci daga Jami’ar Peshawar da ke Pakistan, da kuma digirin digirgir (PhD) a Nazarin Addinin Musulunci daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
Farfesa Usman ya taɓa zama Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, kuma fitaccen malamin addinin Musulunci ne.
Gudanarwa da ma’aikatan NAHCON sun yaba da gudunmawar Farfesa Usman ga alhazan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar NAHCON ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka masu sauƙi da mayar da hankali ga jin daɗin alhazai, tare da shirye-shiryen tabbatar da nasarar gudanar da Hajjin 2026.

