Kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 na tafiya yadda ya kamata, duk da karuwar rikice-rikicen siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jakadan Saudiyya a ƙasar Indonesia, Faisal bin Abdullah Al-Amudi, ne ya bayar da wannan tabbacin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jakarta.
Ya ce, “Alhamdulillah, Saudiyya na cikin aminci a halin yanzu, kuma komai zai gudana kamar yadda aka tsara,” yana mai nuna kwarin gwiwa kan yadda hukumomi suka shirya karɓar miliyoyin alhazai.
A cewarsa, dukkan shirye-shiryen Hajji na tafiya daidai da tsare-tsaren da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa, ba tare da wani tangarda daga halin da ake ciki a yankin ba.
Ya ƙara da cewa muhimman shirye-shirye kamar sufuri, masauki da sauran ayyukan kula da alhazai ana tafiyar da su bisa ƙa’idoji domin tabbatar da sauƙin gudanar da ibadar.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali a wasu sassan Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya jawo damuwa ga wasu maniyyata daga ƙasashe daban-daban, ciki har da Indonesia wadda ke da ɗaya daga cikin mafi yawan alhazai a duniya.
Jakadan ya jaddada cewa babu dalilin fargaba, domin tsaro a Saudiyya yana nan daram, kuma halin da ake ciki bai shafi shirye-shiryen Hajji ba.
Haka kuma ya tabbatar da cewa jiragen da za su ɗauki alhazan Indonesia za su tashi bisa jadawalin da aka tsara, tare da cikakken shiri domin tabbatar da tafiya cikin aminci zuwa da dawowa daga Saudiyya.
Ya tunatar da cewa tun daga ranar 13 ga Maris, shirye-shiryen Hajjin 2026 ke gudana cikin nasara ba tare da wata babbar matsala ba.
A ƙarshe, ya ce gwamnatin Saudiyya na ci gaba da bai wa tsaro, jin daɗi da walwalar alhazai muhimmanci, tare da haɗin gwiwa da ƙasashe abokan hulɗa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin gaba ɗaya.

