Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya jaddada kudirin hukumar na gina wani tsari mai juriya da hada-hadar kudi na ayyukan Hajji a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsaki na harkar Hajji da Umrah na Najeriya karo na biyu da aka gudanar a otal din Nicon Luxury Abuja, Farfesa Usman ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin dandali na tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar Hajji. Taron ya nuna bayyanarsa ta farko a irinsa tun bayan hawansa mulki.
Taron mai taken “Dorewar Kudaden Aikin Hajji: Samar da ci gaba ga Alhazai da Ma’aikata na Najeriya”, taron ya hada masu ruwa da tsaki daga gwamnati, cibiyoyin addini, cibiyoyin kudi, masu kamfanonin jirgin yawo, da kungiyoyin farar hula.
Farfesa Usman ya yabawa Cibiyar bayar da horo kan ayukan Hajji ta Najeriya (HIN) da ta shirya taron tare da jinjinawa bankin Jaiz Plc da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da suka dauki nauyin shirin.
Ya kuma jaddada bukatar samar da tsarin kudi mai dorewa bisa la’akari da hauhawar farashin aikin Hajji saboda rashin canjin kudaden kasashen waje da kuma sauya salon tafiyar da harkokin mulki.
Da yake karin haske kan babbar nasarar da aka samu, Shugaban Hukumar NAHCON ya sanar da shigar da sabbin bankunan hadin gwiwa guda uku – Alternative Bank, Bankin TAJ, da Bankin Lotus – cikin shirin Adashin gata mai dogon zango na Hajj Savings Scheme
A yayin Taron, tsohon mataimakin shugaban bankin raya Musulunci, Dr. Mansur Muhtar,ya gabatar da jawabi , dan kuma gudanar da zaman tattaunawa karkashin jagorancin kwararrun da suka hada da Bashir M. Bugaje, Dr. Muhammad Ahmad, da Farfesa Wasiu O. Gadaeen.
Farfesa Usman ya tabbatar wa masu ruwa da tsakin shirin NAHCON na shirin gudanar da aikin Hajjin 2025, inda ya bayyana cewa an baiwa wasu kamfanonin jiragen sama hudu lasisin jigilar maniyyata sama da 40,000, baya ga fiye da 14,000 da ake sa ran za su bi kamfanonin jirgin yawo
An shirya tashin farko alhazai a ranar 9 ga Mayu, 2025.
Ya bayyana matukar godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima bisa goyon bayan da suka ba su, musamman wajen janye batun bayar da guzuri ta ATM shawarar da ta kawo sauki ga mahajjata da masu gudanar da aikin.
Shugaban Hukumar NAHCON ya kuma mika godiyarsa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar bisa jagorancinsa da goyon bayansa, sannan ya nuna godiya bisa sadaukarwar da mambobin Hukumar da ma’aikata da kuma shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi suka yi.
Farfesa Usman ya kammala jawabinsa da alkawarin jagorantar NAHCON bisa gaskiya, sadaukarwa, da tsoron Allah.