Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kebbi Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammadu Ilyasu Bashar, ya karamma Shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta ƙasa Malam Jalal Ahmad Arabi da sarautar (ƊAN BURAN GWANDU BABBA)
Da yake jawabi a madadin mai martaba sarkin Gwandu Alh Aminu Ahmad SFADA Sarkin Fadan Gwandu ya bayyana cewa mai martaba sarkin Gwandu ya amince da bayar da wanan karammawa ga malam Jalal ne a bisa jajircewa da kuma taimako da yake yiwa Alhazzan Nijeriya tare da haɗin kai da yake bawa shugabani akan abinda ya shafi harkar aikin Hajji mussaman a bana.
Shima Shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu ya bayyana jin daɗin shi matuƙa akan wanan karammawar da akayi ma maigidan shi a masarautar shi ta Gwandu ya kuma yabawa mai martaba sarkin Gwandu Mej.Gen.Muhammadu Ilyasu Bashar akan yadda yake gabatar da kyakkyawan jagoranci zuwa ga Al’ummar Gwandu.

Wannan bayar da takardar karramawa ta sarautar (ƊAN BURAN GWANDU) Sun haɗa da. Alh Aminu Ahmed SFADA Sarkin Fadan Gwandu. Alh Aminu Abubakar Gulumbe Uban ƙasar Gulumbe. Alh.Mustapha Ka’oje Sarkin Bargun Ka’oje. Alh Lamiru Shehu Sakataren Sarakunan jihar Kebbi. Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu. Alh Usman Osho da Alh Rilwanu Awwal.
Shugaban hukumar Alhazan ta kasa, Malam Jalal Muhammad Arabi ya bayyana jin daɗin shi sossai ganin wanan karramawa da ya samu daga masarautar Gwandu ya kuma ce jihar Kebbi ta zama gida a gareshi ganin yadda yake samun karramawa da mutuntawa a jihar ya kuma bayyana mana irin mutunci da zumunci dake tsakanin shi da shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu ya kuma yi godiya da jinjina zuwa ga Maigirma Gwamnan jihar Kebbi His Excellency Comrd Dr Nasir Idris Ƙauran Gwandu akan irin yadda yayi ɗawainiya ga Alhazzan jihar shi.