A wani yunkuri na zurfafa hulda da masu ruwa da tsaki, tawagar gudanarwar hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta ziyarci Oba na Legas, Oba Rilwan Babatunde, a fadarsa
A yayin ziyarar, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya jadadda muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen wayar da kan alhazai kan ayyukan Hajji da kuma ayyukan da suka rataya a wuyansu.
Ya kuma nemi goyon bayan sarkin wajen wayar da kan al’ummar musulmi kan shirin ceto aikin Hajji, inda ya bayyana muhimmancinsa wajen magance kalubalen da ke da alaka da ayyukan Hajji a Najeriya.
A nasa jawabin, Oba Rilwan Babatunde ya nuna jin dadinsa da ziyarar tare da yabawa kokarin NAHCON.
Ya kuma bukaci shugaban hukumar da tawagarsa da sauran masu kula da aikin Hajji da su tabbatar da ayyukansu sun yi daidai da koyarwar addinin Musulunci, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a ayyukansu.
Ziyarar wani mataki ne a kokarin NAHCON na samar da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen ciyar da aikin Hajji gaba a Najeriya.