Rahotanni da Kungiyar Hajj Media Support Professionals (AHMSP) suka samu, sun nuna cewa, shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi maraba tare da bayyana godiya mai tarin yawa da farin ciki kan gaggawar umarnin da Mai girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na yin ragi farashin kudin Hajji na shekarar 2026.
Wannan umarni dai ya yi daidai da hangen nesa da manufa ta Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wato tabbatar da Hajji mai rahusa ga ‘yan Najeriya.
Za a iya tunawa, kusan makonni biyu da suka gabata, Hukumar Alhazai ta Kasa ta sanar da farashin kudin Hajji na 2026, wanda ya dan yi kasa kadan da na shekarar 2025, bayan tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.
Yanzu dai, burin shugaban NAHCON na ganin farashin kudaden Hajji ya zama mai sauki ga alhazai ‘yan Najeriya yana kara samun nasara.
Kididdigar Dalar Amurka da aka yi amfani da shi wajen kirga farashin kudaden Hajjin shi ne Naira 1,550 da dala daya, duk da cewa darajar Naira ta kasance tana karuwa a cikin ‘yan makonnin nan. Sai dai, farashin da aka sanar da farko ba zai rasa nasaba da tsoron canjin kasuwar Dala da kuma tabarbarewar yanayi, wanda ya saba faruwa a cikin shirye-shiryen Hajji a Najeriya tsawon shekaru.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya gode
wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, bisa wannan mataki na kishin al’umma.
A karshe, Farfesa Sale ya yi kira ga Musulman Najeriya da su ci gaba da yin addu’a sosai domin nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu, yayin da ake jiran sabon farashin kudaden Hajji da za a sanar nan gaba kadan.