Shugaban riko na Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale, ya jagoranci taron Shugabannin hukumar na farko.
Taron wanda ya gudana a daidai lokacin da muke hada wannan rahoto, ya samu halartar manyan jami’ai da suka hada da Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Watsa Labarai da dakin karatu(PRISLS), Prince Anafi Elegushi, Kwamishinan Ayyuka (DILU), da Prince Alju Abdul Razaq, Kwamishinan Kuɗi (PPMF). Dr. Saleri Usman Muhammad, mataimaki na musamman ga shugaban na riko
A jawabinsa na bude taron, Farfesa Sale ya nuna godiya ga Ubangiji da ya ba shi damar hidimtawa bakin Allah.
Ya kuma jaddada muhimmancin magance muhimman batutuwan da aka gabatar a yayin taron da ya gabata, yayin da yake addu’ar Allah ya yi masa jagora ya tabbatar da tattaunawa mai amfani.
(DANDALIN SADA ZUMUNTA NA NAHCON)