A ‘yan kwanakin nan ne dai wasu ’yan tsirarun mutane da ake ganin sun fi son biyan bukatun kansu fiye da na amfanin gama-gari maniyyatan Nijeriya (NAHCON) sun yi ta zarge-zarge a kan Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).
Karanta Labari Makamancin Wannan: Yadda Farfesa Abdullahi Sale Ya Kawo Sauyi A Harkokin Aikin Hajjin Najeriya – Daga Nura Ahmad Dakata
Amma muna tambayar me ya sa duk wannan ƙiyayya? Shin shugaban Hukumar ya karya dokar da ta kafa hukumar NAHCON? Shin an same shi da wani laifin cin hanci da rashawa?
Amsar tambayoyin biyu ita ce a’a. Wadannan zarge-zargen ba komai ba ne illa maras tushe, barna, da kuma kokarin yunƙurin yaudarar hankalin jama’a.
A cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar Kwararrun ‘yan jaridu masu tallafawa alhazai ta Najeriya Nura Ahmad Dakata ya sanya hannu, ya ce, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya nuna a sarari na yin gyare-gyare, tabbatar da gaskiya da kuma inganta ayyukan Hajji a Najeriya baki daya.
Jagorancinsa ya kawo kwarewa da hankali ga tsarin da, a baya ya lalace ta hanyar rashin aiki da bukatun son kai.
Mu fayyace: Aikin Hajji ibada ce ta addni ba sana’ar kasuwanci ba.
Hukumar da ke karkashin jagorancin Farfesa Usman tana aiki tukuru don tabbatar da ganin ta tsarkake aikinta.
Sai dai kuma abin takaicin shi ne, akwai wasu a ciki da wajen tsarin da suka fi son mayar da aikin Hajji tamkar wata riba ta masu kallon duk wani gyara a matsayin barazana ga bangarensu.
Zasu iya kokarin yin yaki na batanci da karya, amma ba za su yi nasara ba, insha Allahu. Gaskiya za ta tsaya tsayin daka, komai yawan karairayi.
Maimakon tallafawa kokari don inganta aikin Hajji, ya zama mai araha, da kuma samun lada ga mahajjatan Nijeriya, waɗannan “marasa kishin addininsu” sun zaɓi hanyar yin zagon ƙasa.
Amma al’ummar Musulmin Najeriya ba makafi ba ne. Irin gagarumin goyon bayan da ake baiwa shugaban na yanzu daga masu ruwa da tsaki na gaskiya ya nuna kwarjininsa da hangen nesansa.
Muna kira ga al’umma musamman wadanda suka damu da makomar ayyukan Hajji a Najeriya da su yi watsi da hayaniyarsu, su kuma yi watsi da suruntun karyarsu.
Makiya ci gaba na iya kara kururuwa, amma ba za ta je ko’ina ba.
Ba me ce Farfesa Abdullahi Saleh Usman ba ya laifi ba, amma mai gaskiya ne, da hankali, kuma mai bin ka’idojin adalci da rikon amana ne.
Irin shugabancin da NAHCON ke bukata kenan a yanzu fiye da kowane lokaci.