Darakta Janar na Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya fara rabon muhimman kayayyakin aikin Hajji ga alhazan jihar da za su tafi kasa mai tsarki.

 

Karanta Labari makamancin wannan: Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Kano Ta fara Aikin Samar Da Biza Ga Maniyyata

 

Alhaji Lamin Rabi’u ya bukaci dukkan masu shirin zuwa aikin Hajji da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya kamata, tare da kaucewa daukar wasu kayayya da hukumar kasar Saudi Arabia ta haramta

 

Haka kuma, ya umurci dukkan alhazai da su tuntuɓi jami’an aikin Hajji na kananan hukumominsu domin karɓar kayayyakin.

 

Bugu da ƙari, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), da ta sake duba batun amfani da katin ATM wajen bayar da kudin alhazai. Ya jaddada bukatar bayar da kuɗaɗen tafiya (BTA) a matsayin kuɗi na hannu domin sauƙaƙa wa alhazai samun damar amfani da su.

 

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar, Daraktoci na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya shawarci alhazan da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya dace.

 

Kayayyakin da ake rabawa sun haɗa da: jakunkunan hannu, kayan suttura na maza da na mata, hijabai, zobunan hannu , da kananan jakunkuna domin ajiye kuɗi da muhimman takard

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version