Aikin jigilar maniyyata Hajji daga Pakistan ya fara ne a ranar Asabar, inda alhazai 1,357 suka isa Prince Muhammad bin Abdulaziz Airport.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Pakistan ta ce Saudiyya ta ba ta karin kujerun aikin Hajji 10,000
Jakadan Pakistan a Saudiyya, Ahmed Farooq, tare da Babban Jakadan ƙasa (Consul General) Syed Mustafa Rabbani da Darakta-Janar na Hajji Abdul Wahab Soomro, sun tarbi alhazan a filin jirgin sama. Sauran jami’an aikin Hajji na Pakistan ma sun halarta domin kula da shigowar maniyyatan.
Bayan isarsu, an kai alhazan zuwa yankin Markaziyah, kusa da Masjid al-Nabawi, inda aka tanadi masauki ga dukkan alhazan 119,210 da ke karkashin shirin gwamnati na bana. Jami’ai sun tabbatar da cewa an riga an ware ɗakuna tun kafin zuwansu, domin su samu sauƙin shiga ba tare da jinkiri ba.
Haka kuma, an raba musu katin Nusuk, wanda ake buƙata domin shiga wuraren ibada da gudanar da ayyukan Hajji. Bayan haka, an shirya musu abincin tarba.
Bayan sun huta, alhazan sun nufi Masallacin Annabi domin yin sallah da kuma kai gaisuwa ga Annabi Muhammad (SAW), wanda yawanci shi ne matakin farko da mafi yawan alhazan ke yi bayan sun isa Madinah.
Ɗaya daga cikin alhazan ya yaba da yadda aka shirya komai, yana mai godiya ga gwamnatocin Pakistan da Saudiyya bisa kyawawan tsare-tsaren da suka yi.
Ana sa ran karin jirage dauke da alhazan Pakistan za su ci gaba da isowa a kwanaki masu zuwa, yayin da wannan aikin jigilar kafin babban lokacin Hajji ke ci gaba.
(II)
