A cikin wani bincike da ake gudanarwa kan bata sunan da aka yi wa Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta hannun wasu kafafen yada labarai kwanan nan, wannan sanarwa na zuwa ne domin fayyace abubuwan da suka fito fili da kuma kare martabar Shugaban Hukumar da sauran jagorancinta.

Shaidu sun tabbatar da cewa rahotannin batanci da ake yadawa a kafafen yada labarai ba daga aikin jarida na gaskiya suka samo asali ba, illa wani shiri ne na musamman da aka tsara domin bata sunan shugabancin NAHCON tare da karkatar da hankalin jama’a. Binciken ya nuna cewa Hukumar na ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya, rikon amana da kwararewa, duk da yunkurin da ake yi don gurbata aikinta.

A cikin Binciken da ya gudanar, wani fitaccen dan jarida mai gudanar da bincike mai zaman kansa a Abuja mai suna K A Kontagora,  ya gano cewa akwai wata kungiya ta ’yan jarida, tsofaffin jami’an hukumar da wasu ma’aikatan hukumar marasa kishi da suke rubuta da kuma yada rahotannin karya a kai a kai domin matsawa Gwamnatin Tarayya lamba ta sauya tsarin jagoranci a NAHCON.

Wadannan rahotanni sun yi kama da juna ta fuskar salo da lokaci, tare da samun bayanai cewa ana rubutasu ne a wasu kungiyoyin tattaunawa na sirri kafin a turasu zuwa wasu kafafen yada labarai. An kuma gano cewa an boye kudaden da ake bai wa wasu a matsayin “Tallafin rubutu” ko “Kudin aikin musamman”, lamarin da ya nuna cewa kamfen din ciniki ne kawai, ba wai aikin jarida na gaskiya ba.

Wani bangare na binciken ya nuna cewa akwai hada-hadar cikin gida da na waje, inda aka rika fitar da takardu, yada jita-jita da karkatar da bayanai domin kirkirar labaran bogi. Daya daga cikin manyan karya da aka dinga yadawa  batun cin rashuwar naira biliyan 50  tuni an tabbatar da karya ce bayan duba takardun binciken kudi na zahiri.

Binciken ya tabbatar da cewa ayyukan kudi na NAHCON suna gudana bisa ka’idojin gwamnatin tarayya, kuma babu irin wannan ma’amala ko tangarda. Wasu gidajen yada labarai ma sun ki karbar kudaden da aka ba su domin yada labaran karya saboda rashin dacewar abin da ake son su wallafa, abin da ya nuna cewa akwai ’yan jarida masu mutunci da har yanzu suke kiyaye ka’idojin aiki.

Binciken ya kuma gano tsari mai tayar da hankali, inda ake amfani da bayanan karya domin tada hankalin jama’a, karkatar da hankulan mutane daga gaskiya, tare da neman tada jijiyar wuya a muhimman hukumomi.

Da dama daga cikin wadanda suka shiga wannan mummunan shiri sun kasance masu kare NAHCON a baya, amma yanzu sun koma masu sayar da kansu ga duk mai bayar da kudi, ba tare da la’akari da ka’ida da mutuncin aikin jarida ba. Manufofinsu sun hada da rushe amincewar da ake da ita ga hukumar da kuma kokarin shafar yanke shawara a bangaren aikin Hajji domin cimma manufofinsu na kashin kai ko na siyasa.

Yayin da binciken ke ci gaba, hukumar binciken ta yi kira ga jama’a da kafafen yada labarai su dogara ne kawai kan bayanan da aka tabbatar ta hannunta, tare da kiyaye ka’idojin aikin jarida. Shugaban Hukumar NAHCON da tawagarsa za su ci gaba da maida hankali wajen gudanar da aikinsu na kula da alhazai da inganta tsarin gudanar da aikin Hajji a Najeriya.

Za a ci gaba da fitar da wasu bayanan da suka shafi wadanda ke da hannu, wadanda suka dauki nauyin kudi da wadanda ke ba su bayanan cikin gida nan gaba, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a idon jama’a.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version