A Najeriya, jita-jita kan zama kamar gaskiya idan aka yi ta maimaitawa. Labaran karya kan shafe na gaskiya, saboda mutane suna son jin labaran Al’ajabi, shakku ko mamaki. Mun taba jin labarin Madam Koi-Koi da Iliya dan Mai-Karfi, duk da ba gaskiya ba ne, amma mutane sun dade suna yada wannan labaran.

Yanzu haka, Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON, da Shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman, sun fada cikin irin wannan jita-jitar. Zargin wai an sace Naira biliyan 50 a hajjin da ya gabata. Labarin ya yadu Kamar wutar daji a kafafen sada zumunta da jaridu, amma babu wata hujja ko gaskiya cikin lamarin. Zargi ne kawai da ‘Yan siyasa ke kara rura wutarsa.

Idan muka duba lamarin a hankali, za mu ga cewa wannan magana bata da tushe. A 2025, alhazai daga kudanci sun biya kusan Naira miliyan 8.78, yayin da na arewa suka biya Naira miliyan 8.46. Idan aka raba Naira biliyan 50 da wannan farashi, zai bamu adadin alhazai kusan 5,700. Wato sai mutum ya karbi kudin alhazai fiye da dubu biyar da ba su tafi Hajji ba, ko kuma ya karkatar da kaso 12 na kudin dukkan alhazai suka Biya a kasar sannan hakan za ta iya kasancewa.

Irin wannan satar ba abu ne mai sauki ba. Domin sai NAHCON da masu jiragen sama da masu masauki da masu abinci, da hukumomin jihohi su hada baki lokaci guda, kafin a iya cin wadannan kudade.

Sai kuma a ce irin wannan kudi sun bata amma majalisar wakilai da fadar shugaban kasa su yi shiru gaba daya. Wannan kusan ba zai taba yiwuwa ba.

A yau, babu wata Shaida da ta nuna an saci irin wannan kudi. Babu wanda ya fito da takarda ko shaidar batan kudin. Babu kasafin kudi wato (budget) da ya nuna wani gibi na wannan kudade Amma kawai sai labari keta yaduwa, domin mutane na son jin irin wadannan jita-jita.

Abin da nake gani a  Najeriya ce kawai hakan ke faruwa. Idan sabon shugaba mai son ayi gyara ya hau, sai ya fara gyare gyare. Wadanda suka saba da tsohon tsarin sukan ji haushi, su fara yada jita-jita don su bata sunan sabon shugaban. Sai a shaci labarin teburin Mai Shanyi a  fitar da adadin kudi mai yawa kamar “biliyan 50” don ta tada hankali da kawo CeCe-kuce a tsakanin jama’a

Gaskiya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman yana kokarin tsaftace aikin Hajji. Ya rage almundahana, ya kara tsari. Wadannan canje-canje suna bawa wasu ciwon kai, musamman wadanda suka saba cin moriyar tsohon tsarin.

Amma fa, wannan ba yana nufin kada ayi a bincike ba. Idan akwai laifi, a bincika a fito fili dashi. Mutane na da hakkin sanin gaskiya. Amma su ma Yan NAHCON suna da hakkin kada a zalunce su da jita-jita marar hujja.

Har yanxu Hukumar EFCC ma bata fitar da wata shaida ba. Babu rahoton da ya tabbatar da wannan zargi. Abin da ke yawo kawai shi ne maganar “an sace biliyan 50,”

NAHCON tana da lissafi. Ana iya duba adadin alhazai, kwangiloli, da kudade. Idan akwai rashin gaskiya, sai a gani a rubuce. Wannan shi ne ainihin hanyar bincike, ba hira a Facebook ko WhatsApp ba.

Madam Koi-Koi bata taba wanzuwa ba, amma har yanzu mutane na jin labarinta. Haka ma wannan labari na biliyan 50, ya yadu ne saboda mutane sun riga sun yarda cewa gwamnati tana cike da rashawa. Amma imani ba hujja ba ne. Kuma gwamnati ba za ta yi aiki a bisa zato cewa kowa barawo ba ne.

A bari masu bincike su gama aikinsu. A bari gaskiya ta fito fili. Jama’a su nemi gaskiya da adalci, domin duka biyun suna aiki tare.

Gaskiya tana da daraja fiye da jita-jita. Kada mu bar karya ta maye gurbin gaskiya.

Ganiyu Lamidi
Masani ne kan manufofin gwamnati da gyaran gudanarwa a Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version