Ministan Harkokin kasashen Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yabawa Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, bisa hangen nesa da kokarin da ya yi na aiwatar da tsare-tsare na inganta jin dadin Alhazan Najeriya.
Ambasada Tuggar ya yi wannan furucin ne yayin wata tattaunawa ta da Jaridar Hajj Chronicles daga birnin Abu Dhabi
Ya bayyana irin gagarumin ci gaban da NAHCON ta samu a karkashin jagorancin Farfesa Saleh, inda ya jaddada cewa wadannan matakai sun kara habaka aikin Hajji da Umrah ga maniyyata a fadin kasar nan.
Ministan ya bayyana cewa tun lokacin da aka nada shi, Farfesa Saleh ya rika tuntubarsa domin neman shawarwari.
Ya bayyana wannan matakin a matsayin shaida na jajircewar Shugaban Hukumar da kuma dabarun da ko shakka babu za su karawa Hukumar NAHCON damar gudanar da ayyukanta cikin inganci.
Ministan ya kuma amince da matakan da hukumar NAHCON ta dauka na tunkarar kalubale a fannin da kuma tabbatar da gudanar da ayyukan hajji cikin sauki.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa wadannan yunƙurin za su ci gaba da ƙarfafa martabar Nijeriya a harkokin Hajji da Umrah na duniya.
Ambasada Tuggar ya kara jaddada kudirin gwamnatin tarayya na mara baya ga hukumar NAHCON a kokarinta na samar da ayyuka masu inganci ga alhazan Najeriya.
Ya bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da baiwa Hukumar da sauran masu ruwa da tsaki hadin kai wajen ganin an samu ci gaba a aikin hajji.
Idan za a iya tunawa a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025 shugaban NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Usman ya rattaba hannu da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025 a madadin ministan harkokin wajen Najeriya. , wanda bai samu damar halarta ba saboda wasu muhimman ayyukan da suka tafi da shugaban kasa zuwa birnin Abu Dhabi.