Daga Mariam Zubair Abubakar

 

Kwamishinan ayyukan Haji, Prince Anofie Olarenwaju Elegushi shi ne ya kaddamar da kwamitocin guda  biyu domin tantance aikace-aikace da kuma duba ofisoshin kanfanonin masu gudanar da ayyukan Haji da Umrah

 

Alhaji Alidu Shutti ne zai jagoranci kwamitin tantance aikace-aikacen, sannan kuma kwamitin duba ofisoshi na kasa zai kasance karkashin jagorancin Alhaji Abdul-Ghaffar.

 

Bisa ga dokar NAHCON ta 4, sashe na 1, kamar yadda kwamishinan ya bayyana, hukumar na da alhakin bayar da lasisi, tsarawa, kulawa, da gudanar da ayyukan sa ido kan kamfanoni, kungiyoyi ko makamancinsu masu gudanar da ayyukan Hajji da Umrah.

 

A cikin jawabinsa, Kwamishinan ya tunatar da kwamitocin muhimmancin su wajen gudanar da irin wannan muhimmiyar rawa da kuma wakilcin hukumar. Dangane da haka, ya bukace su da su kasance masu gaskiya, kuma su gudanar da ayyukansu ba tare son zuciya ko kuma takurawa wani ba.

Ya kuma bayyana cewa duk kamfanonin da aka tantance dole ne su mallaki takardun da ake bukata kafinsu cancanta.

 

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan kwamitin da su kula da lokaci, domin hukumar na bukatar tafiya daidai da kalandar Hajji ta 2025. Ya bukace su da su yi aiki tukuru da inganci don hanzarta aiwatar da dukkan ayyukan don cimma manufofin da ake so.

 

Daga karshe ya yi musu fatan yin aiki lafiya da samun kariya a ziyarar da zasu a yi a fadin kasar nan. Alhaji Elegushi ya kuma tunatar da su cewa za a yi aiki da rahotannin da suka bayar kuma dole ne su kasance sahihai kuma amintattu, domin Hukumar ta dogara dasu.

 

A nasa jawabin, shugaban tawagar duba ofisoshin, Alhaji Abdul-Ghaffar, ya nuna jin dadinsa ga hukumar bisa la’akari da mambobin kwamitin da suka cancanci wannan aiki. Ya yi alkawarin ba da himma da kwazo wajen gudanar da aikin da aka damka musu tare da tabbatar da cewa za su kammala shi cikin wa’adin da aka kayyade.

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version