Dangane da jinkirin wajen sanar da fara rijistar maniyyata da wasu hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi da suke yi, kungiyar masu bayar da rahotanni da sa ido kan harkokin Hajji da Umrah ta Najeriya mai zaman kanta,ta yi kira ga Gwamnonin Jihohin da su baiwa al’amuran Hajji fifiko a Jihohinsu.
“Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari, Jihohin Neja, Sokoto da Borno har yanzu ba su fara aikin rajistar ba duk da cewa sun samu umarnin Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) a watan Agusta na cewa Jihohin su fara rajista.
“Muna sane da cewa har yanzu wasu Sakatarorin zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai Musulmi ba su mika rahoton aikin Hajjin 2024 ga Gwamnoninsu ba, wanda a sakamakon haka har yanzu ba su samu amincewar fara rajistar maniyyata daga shugabanninsu ba,” in ji IHR. a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan ta na kasa, Ibrahim Mohammed, ranar Laraba.
Kungiyar ta fararen hula ta kuma nuna damuwarta kan yadda har yanzu ba a fara rijistar wasu jihohi ba ko da ana sa ran za su mika kaso na farko na kudaden ajiyar maniyyata zuwa hukumar NAHCON, tun daga ranar 2 ga watan Oktoba (kamar yadda kalandar hukumar NAHCON ta 2025 ta nuna) don isarwa ga kamfanonin don biyan kudin tantina a Mina.
“Cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha za ta bukaci wata amincewa ta daban daga Gwamnonin Jihohi don fara rajistar maniyyata ko da bayan an ba su izini daga hukumar kula da aikin hajji, wani shiri ne na musamman na hadin gwiwa ga masana’antar Hajji wanda ke bukatar mafita cikin gaggawa”.
Kungiyar ta ce “Ya zama dole a lura cewa a ranar 23 ga watan Oktoba ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta fara raba tanti ga kasashen da suea halartar aikin Hajji da suka biya.
“Duk wani sakataren zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai Musulmai na Jiha wanda bai gabatar da rahoton aikin Hajjin na 2024 watanni hudu bayan aikin Hajjin 2024 ba to a cire shi tare da maye gurbinsa da wanda ya cancanta,” in ji kungiyar.
Sannan kuma ya tunatar da gwamnonin jihohin cewa jinkirin fara rajistar maniyyata da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi ke yi, shi ne ummul haba’isin matsalar rashin hidima da alhazan Najeriya ke fuskanta duk shekara a Saudiyya.
“Yin ragistar a makare yana haifar da jinkirin tura asusun rijistar maniyyata zuwa NAHCON, wanda hakan ya shafi gazawar hukumar wajen biyan kudade ga kamfanoni dake yin hidima ga alhazai da ke Saudiyya a daidai lokacin da zasu bad a damar yin isassun shirye-shirye don samar da ingantacciyar hidima ga maniyyatanmu.
“Ma’aikatan gudanarwa na jihohi na kawo cikas sosai wajen aiwatar da kalandar Hajji, don haka akwai bukatar a yi wani abu don yin daidai da dokar kafa hukumar NAHCON ta shekarar 2006, don baiwa maniyyatan jihohi damar fara rajista da wuri ba tare da jiran amincewar shugabannin zartarwa na jiha ba.
“Aikin Hajji al’amari ne na duniya wanda ake sa ran sama da kasashe 162 da ke halartar taron za su aiwatar a lokaci daya da aka fitar duk shekara kamar yadda ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta fitar don zama taswirar jagora don shirye-shiryen aikin Hajji,” in ji kungiyar