A wani bangare na shirye-shiryen tunkarar aikin Hajjin shekarar 1447 Hijiriyya, hukumomin Saudiyya sun kaddamar da wasu sabbin shirye-shiryen horaswa domin inganta kwarewar malamai da masu jagorantar maniyyata.

Shugaban harkokin addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ne ya kaddamar da shirye-shiryen a ranar Juma’a, 1 ga Mayu, 2026, a birnin Madinah.

Shirin farko mai taken “Koyar da Hukunce-hukuncen Hajji” an tsara shi ne tare da hadin gwiwar Majalisar Manyan Malamai, inda ake koyar da fikihu da ka’idojin aikin Hajji, tare da gabatar da laccoci daga manyan malamai.

Al-Sudais ya bayyana cewa manufar shirin ita ce kara inganta kwarewar masu wa’azi domin su iya jagorantar maniyyata yadda ya kamata, musamman a lokutan cunkoso. Ya kuma jaddada cewa hadin gwiwar na nufin yada sahihin ilimin addini cikin tsaka-tsaki da daidaito.

Haka kuma, an kaddamar da wani shiri na biyu mai taken “Koyar da Ayyukan Hajji Ga Limaman Masallatai Biyu Masu Tsarki,” wanda ake gudanarwa a Al-Masjid an-Nabawi. Shirin ya shafi limaman Masjid al-Haram da na Masallacin Annabi, inda su kansu limaman ke gabatar da laccoci.

Ya ce wannan horaswa na daga cikin kokarin tabbatar da cewa limamai sun samu cikakken ilimi kan aikin Hajji tare da inganta yadda suke isar da sakonni ga maniyyata.

Wadannan shirye-shiryen na daga cikin manyan tsare-tsaren ilimi da ake yi kafin fara aikin Hajji, domin tabbatar da ingantacciyar jagoranci ga miliyoyin maniyyata da ake sa ran za su halarta a shekarar 2026.

(II)

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version