Majalisar Ministoci ta ƙasar Saudiyya ta amince da wani tsari na wucin gadi na ɗaukar nauyin dukkan haraji da kuɗaɗen kwastam da ake ɗora wa dabbobin da ake shigowa da su cikin ƙasar a lokacin Hajjin 1447H.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Hukumar Alhazai Ta Jahar Sokoto Ta Kammala Dukkanin Shirye-Shiryen Hajin 2026 A Saudi Arabia
Wannan mataki zai fara aiki daga 1 ga watan Zul Qi’ada 1447H (18 ga Afrilu, 2026) har zuwa ƙarshen aikin Hajjin shekarar, domin sauƙaƙa shigo da dabbobin da ake buƙata wajen gudanar da ibadar Hajji.
A karkashin wannan tsari, gwamnati za ta biya dukkan kuɗaɗen da suka shafi shigo da dabbobi kamar tumaki, awaki, shanu da raƙuma. Ana sa ran hakan zai rage matsin lamba ga ‘yan kasuwa da kuma ƙara wadatar dabbobin hadaya.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin da hukumomi ke yi na daidaita hauhawar buƙatar dabbobi a lokacin Hajji, musamman don ibadar Hadaya (Hady), wadda ke zama wajibi ga wasu mahajjata.
Ta hanyar ɗaukar wannan nauyi, gwamnati na nufin daidaita farashin dabbobin hadaya, inganta tsarin samar da su, da kuma bai wa mahajjata damar sauƙin gudanar da ibadunsu ba tare da tsadar da ba dole ba.
Haka kuma, an umurci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da wannan tsari cikin sauƙi, tare da hanzarta fitar da dabbobin da ake shigowa da su a dukkan mashigai na ƙasar.
