Tsarin gaskiya da tsantsaini da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bi, wajen raba kudade ga dukkan hukumomin jin dadin alhazai na Jihohi domin mayar da kudaden da suka samu a aikin hajjin 2023, a matsayin diyya ga ayyukan da ko dai ba ayi musu da kyau ba, ko kuma ba ayi yi musu gaba daya bag a dukkanin kamfanoni masu yi wa alhazai hidima a Minaa da Arafat, abu ne da ya kamata a yaba wa hukumar.
Hakika matakin da hukumar NAHCON ta dauka na gaggauta sakin kudaden, inda duk mahajjatan 2023 da abin ya shafa za a tura musu a asusun ajiyarsa na banki Riyal 150 kwatankwacin (N61,080) ta hannun hukumomin alhazai na jahohinsu, tabbas ta cancanci yabo na musamman daga ƴan ƙasa waɗanda ke bibiyar al’amura da abubuwan da ke faruwa a harkar aikin Hajjin Najeriya.
Bugu da kari, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya nunawa masu suka cewar basu fahimci hakikanin gaskiyar lamari ba ta fuskar nuna halin gaskiya, rikon amana da kwarewa, mafi girman lamari kuma shi ne rike al’amuran hukumar alhazan ta kasa ta hanyar tsantsaini
Sai dai a yanzu ya ragewa Hukumomin Alhazai na Jihohi daban-daban kan yadda lamarin ka iya kasancewa don tabbatar da gaggauta mayar da kudaden ga daukacin alhazai wadanda suka gudanar da aikin Hajin 2023 a Jahohinsu.