Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Gombe ta gudanar da bikin rufe Bitar wayar da kai da ilimantarwa na wannan shekara a ranar Lahadi, inda ta bukaci duk maniyyata da su rungumi koyarwar da suka samu yayin da suke shirin tafiya kasa Mai Tsarki.
A jawabinsa ga mahajjata a wajen bikin, Sakataren Hukumar Jin dadin Alhazai Alhaji Saad Hassan, ya jaddada muhimmancin bin doka da ƙa’idojin tafiye-tafiye na Hajji, musamman cikakkun takardu da katin shedar Allurar Rigakafi wato Yellow Card. Ya ce wajibi ne mahajjaci ya kasance yana dauke da takardun tafiya wato Passport da shaidar rigakafi a kowane lokaci, kasancewar hukumomin Saudiyya sun kara tsaurara matakan tantancewa a bana.
Alhaji Saad ya yi gargaɗi ga wadanda suka biya kuɗin Hajji ta kamfanonin masu zaman kansu da su kauracewa guraren allurar rigakafin da hukumar ke gudanarwa. Ya bayyana cewa allurar rigakafin da hukumar ke bayarwa na musamman ne kawai ga wadanda suka biya kuɗin Hajji ta hanyar hukumar Jihar Gombe ko Bankin Ja’iz.
Ya kara da cewa hukumar za ta kara ƙaimi wajen hana mata masu juna biyu tafiya Hajji a bana, duba da abin da ya faru a shekarun baya inda wasu mata suka haihu a ƙasar Saudiyya, wanda hakan ya janyo cikas da matsaloli na lafiya da tsari. Haka kuma, ba za a bar masu fama da matsalolin lafiya masu tsanani su tafi Hajji ba.
Sakatare ya kuma yi kira ga ‘yan uwa da dangi da su dauki alhakin hana tura tsofaffi ko marasa lafiya zuwa kasa mai tsarki sai dai idan akwai wanda zai iya kula da su. “Idan har zai yiwu, ku biya kuɗinku tare da nasu domin ku taimaka musu a kasa mai tsarki,” in ji shi.
Dangane da batun Kudin Tafiye-tafiye na Hajj (BTA) Alhaji Saad ya tabbatar wa mahajjata cewa Gwamnatin Jihar Gombe tare da hukumar sun dauki matakan da suka dace don ganin an guje wa irin matsalolin da suka faru a shekarar 2024, inda Babban Bankin Najeriya ya kasa cika alkawarin bayar da dala 500, inda aka bai wa mahajjata dala 400 kacal.
Domin gyara hakan, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Gombe ta dauki nauyin ganin kowanne mahajjaci ya samu cikakken dala 500 a bana. Haka kuma, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da bayar da goron Sallah ta musamman har Riyal 200 ga kowanne mahajjaci, tare da shirin samar da abinci na musamman a lokacin zama a Arafat.
Alhaji Saad ya kuma bukaci mahajjata da su biya kuɗin Hadaya (layya) ta hannun jami’an Hajji na ƙananan hukumominsu, ko ta ofishin hukumar a Gombe, ko kuma ta bankin Ja’iz, domin tabbatar da tsari da kare mahajjata daga fadawa hannun masu damfara.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar kuma Sarkin Dukku, Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Haruna Rasheed, ya yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar kammala shirin horar da mahajjata na bana cikin nasara. Ya mika godiyarsa ta musamman ga Gwamna Inuwa Yahaya saboda goyon bayan da ya bayar, musamman wajen samar da masaukai masu kyau kusa da Harami a Makkah, wanda ya ce ya zama ɗaya daga cikin mafiya inganci ga mahajjatan Najeriya.
Sarkin ya ce mataki na gaba shi ne hukumar ta tabbatar da aiwatar da duk shirye-shiryen da suka tsara don ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2025. Ya nuna kwarin gwiwa cewa mahajjatan Jihar Gombe za su kasance masu biyayya da ladabi a cikin gida da wajen ƙasa.
Ya kuma shawarci mahajjata da su kiyaye kuɗin BTA da aka ba su, yana mai gargadi cewa hukumar ba za ta iya maidawa ko biya wani da ya rasa kuɗinsa ba. “Zama a Saudiyya ba tare da kudi ba abu ne mai matuƙar wahala,” in ji shi.
Sarkin ya kuma ja kunnen mahajjata kan bada aron katin shaida ko kayan da aka raba musu daga hukumar anan Gombe ko wanda hukumomin Saudiyya zasu basu. Ya umurci mahajjata da su rika sanya su a wuyansu a kowane lokaci domin sauƙin tantancewa da kare kansu daga matsala a ƙasar.
A tunda farko a nasa Jawabin, Shugaban Sashen Horo da Wayar da Kai na Hukumar, Malam Maiwada Dahiru, ya yabawa Sarkin Dukku da Sakatare hukumar saboda cikakken goyon bayan da suka bayar. Ya bayyana godiyarsa musamman irin hadin kai da goyin baya da aka basu da damar da gudanar da shirin BITA a fadin jihar cikin sauki.
Malam Dahiru ya bukaci mahajjata da su aiwatar da duk darussan da suka koya a shirin, yana mai jaddada cewa ilimi da ladabi su ne ginshiƙai wajen samun Hajji mai karɓuwa da lada.
Wadanda suka halarci bikin sun hada da manyan jami’an hukumar, mambobin kwamitin gudanarwa, Shugaban Kamfanin Kautal Jude Travel and Tours, da wasu muhimman masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen nasarar shirin.
Bikin ya zama wata muhimmiyar alama ta cika wani muhimmin mataki a shirin tafiya Hajjin 2025, inda Jihar Gombe ta sake nuna aniyarta na tabbatar da lafiya, jin daɗi, da cikar biyan buƙatun ruhin mahajjatanta a wannan tafiya mai tsarki.