Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana alhininta matuƙa kan rasuwar wasu ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu, inda ta bayyana wannan rashi a matsayin babban rashi mai matuƙar sanya damuwa
A cikin wata sanarwar ta’aziyya da mai magana da yawun Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar a madadin yan Hukumar gudanawa, shugabanci da ma’aikatan hukumar baki ɗaya, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, hukumar ta miƙa ta’aziyyarta ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’ila Falgore, bisa wannan mummunan lamari.
‘Yan majalisar da suka rasu su ne Marigayi Sarki Aliyu Daneji, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Aikin Hajji kuma Wakilin Mazabar Kano Municipal, da Marigayi Aminu Sa’ad, Wakilin Mazabar Ungogo.
Hukumar ta bayyana cewa rasuwar ‘yan majalisar biyu babban rashi ne ba ga iyalansu da mazabunsu kaɗai ba, har ma ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da ƙasar Nijeriya gaba ɗaya, duba da irin gudunmawar da suka bayar wajen hidimar al’umma da bunƙasa harkokin majalisa.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar na tausayawa iyalan marigayan, ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, Gwamnatin Jihar Kano da al’ummar jihar baki ɗaya a wannan lokaci na jimami.
Hukumar ta yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya gafarta musu kura-kuransu, ya sanya su a Aljannar Firdausi, kuma ya baiwa iyalansu da al’ummar Jihar Kano juriyar jure wannan babban rashi.
