Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto ta sanar da nasarar kammala ɗora bayanan dukkan mahajjata 2,403 da suka yi rajista daga jihar a kan manhajar E-Track Masar, kafin rufe shafin a hukumance da mahukuntan Ƙasar Saudiyya suka yi.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar Faruku Umar ya fitar, tace Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, ne ya bayyana hakan a yau yayin wani taro da Mataimakan Jami’an Rajistar Hajji daga ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Alhaji Aliyu Musa ya bayyana cewa rufe Masar Portal na nuna fara wani sabon zamani a harkokin Hajji, yana mai cewa mahukuntan Saudiyya tare da haɗin gwiwar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) sun bullo da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da ingantaccen gudanar da Hajjin 2026.
A cewarsa, daga cikin sabbin ƙa’idojin da aka gabatar akwai fitar da tikitin jirgi tun kafin ranar tafiya, domin kowane mahajjaci ya san ranar tafiyarsa, lokaci da wurin tashi a sarari.
Ya yi gargaɗin cewa duk mahajjacin da ya rasa jirgin da aka tsara masa (no-show) zai fuskanci hukunci, domin za a haɗa tikitin jirgi da katin Nusuk ɗinsa ta hanyar tsarin dijital.
Shugaban ya ƙara da cewa a sabon tsarin, mahajjata za su yi tafiya cikin rukuni na mutum 45, inda kowane rukuni zai tashi tare, ya sauka a otal-otal guda a Makkah, Madinah da Masha’ir, sannan su dawo Najeriya tare bayan kammala aikin Hajji.
Ya kuma bayyana cewa sabon tsarin ya wajabta wa NAHCON ɗora bayanan matafiya a manhajar Nusuk Masar aƙalla awa 72 kafin tashin duk wani jirgin da zai ɗauki mahajjata zuwa Saudiyya.
Ya jaddada cewa ba za a amince mahajjaci ya canza rukuni ba bayan an fitar da biza.
Alhaji Aliyu Musa ya tabbatar da cewa Hukumar ta daidaita tsarin rajista domin bin dukkan sabbin ƙa’idojin, don kare jin daɗin mahajjatan Jihar Sokoto da kuma tabbatar da gudanar da Hajji cikin nasara ba tare da tangarda ba.
