Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da ranar 1 ga watan Junairu, 2025, a matsayin ranar rufe karbar kudaden ajiyar maniyyata a jihar.
A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya ce babban Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan a lokacin wani taro da ma’aikatan hukumar da jami’an alhazai na kananan hukumomi da aka gudanar a ofishin sa.
Ya bayyana cewa wa’adin ya yi daidai da kalandar Hajji ta 2025 da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta fitar, wanda ya bukaci dukkan jihohi su mika bayanan maniyyatan zuwa ranar 7 ga Janairu, 2025.
Alhaji Danbappa ya jaddada bukatar bin umarnin don tabbatar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 cikin sauki.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake samun karancin kujerun aikin Hajji a jihar, ya kuma bukaci jami’an alhazai na kananan hukumomi da su kara kaimi wajen cimma burinsu na rabon kujerun.
“Dole ne mu ɗauki sabbin dabaru don haɓaka tallace-tallace da kuma tabbatar da cewa mun cika ayyukanmu cikin ƙayyadaddun lokaci,” in ji shi.
Darakta Janar din ya kuma bukaci maniyyatan da ke da niyyar zuwa aikin Haji su kammala sanya kudin ajiyarsu a ranar 1 ga watan Junairu ko kuma kafin wa’adin ranar, yana mai gargadin cewa rashin biyan kudin zai iya haifar da rashin zuwa aikin Hajjin 2025.
An shawarci jama’a da su kiyaye da wa’adin da aka diba musu domin kaucewa kawo cikas a harkokin aikin Hajji.