Da yake kaddamar da kwamitin, Kwamishinan Sashen Tsare-tsaren bincike, kididdiga, bayani, da ayyukan dakin karatu (PRSILS) na NAHCON kuma Shugaban Kwamitin Kula da Lafiya na Kasa, Farfesa Abubakar Yagawal, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan kwarewar wakilan kwamitin wajen aiwatar da aikin da aka dora musu. Ya tunatar da su cewa an zabe su ne bisa cancanta domin duk sakamakon da za a samu zai zama don amfanin Alhazan Najeriya.  

 

 

Kwamitin ya kunshi kwararrun likitoci, masu tsara manufofi, da sauran masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan dabarun kiwon lafiya na shekara mai zuwa.

 

 

 

A jawabinsa na bude taron, Shugaban Kwamitin, Dokta Saidu Ahmad Dumbulwa, ya sake tabbatar da jajircewar dukkan wakilan kwamitin wajen dacewa da aiwatar da sabbin ka’idojin yadda ya kamata. Ya jaddada cewa sabunta ka’idoji na shekara-shekara ne, kuma ya tabbatar da cewa kwamitin ya shirya tsaf don fuskantar sabbin nauye-nauyen da aka daura masa

 

 

 

“Na yi maraba da ku baki daya, kuma na taya ku murna bisa kasancewa cikin wannan muhimmin aiki. Inshallah, ina da yakinin cewa za ku bayar da gudunmuwa wajen nasararmu. Allah ya taimake mu a duk kokarinmu,” in ji shi.

 

 

 

Dokta Dumbulwa ya nuna godiyarsa ga Kwamishinan tsare-tsaren bisa kaddamar da kwamitin, tare da yaba muhimmiyar rawar da kwararrun likitoci da masu ruwa da tsaki suka taka wajen cimma nasarori a baya. Ya jaddada muhimmancin hadin kai da aiki tare wajen magance batutuwan da aka sanya a gaba, wanda ya hada da:

 

– Duba ka’idojin 2025 da inganta dabarun aiwatarwa.

 

– Yin hasashen da kimanta kudin magunguna da kayan amfani, a gida da wajen kasa.

 

– Daidaita alawus-alawus na likitoci da ma’aunin da duniya ke kai

 

– Yadawa tare da tabbatar da bin sabbin manufofin kiwon lafiya na Saudiyya.

 

– Kafa ingantattun ayyukan gaggawa na lafiya a sansanonin Alhazai tare da goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

 

– Horas da ma’aikatan lafiya da wadanda aka tantance don ingantaccen aikin hajji.

 

– Inganta hadin kai tsakanin hukumomin tarayya da jihohi karkashin jagoranci guda.

 

 

Kwamitin kuma zai mayar da hankali kan kula da batun lafiyar zuciya da sauran batutuwan lafiya tare da tabbatar da bin manufofin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

 

 

 

“Ba wannan ne karon farko da muke daukar irin wannan nauyi ba. A bara, mun fuskanci irin wadannan kalubale kuma mun samu gagarumar nasara ta hanyar hadin kai da kwarewa. Ina da yakinin cewa za mu iya maimaita wadannan nasarori, ko ma mu wuce su,” a cewarsa.

 

 

 

Shugaban Kwamitin ya yi alkawarin samar da dandali don tattaunawa mai ma’ana da cimma sakamako mai amfani. Wakilan kwamitin sun nuna fata mai kyau kan aikin nasu, tare da tabbatar da cewa za a tsara manufofin lafiya da kuma tabbatar da aiwatar da ka’idojin lafiya na 2025 cikin lokaci don Aikin Hajjin 2025.

 

 

.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version