Sannu a hankali Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) tana ganin wasu sauye-sauye masu amfani da suka dace da tsarin gudanarwa na duniya, karkashin kulawar shugabanta, Farfesa Abdullahi Sale Usman, duk da nufin inganta aikinta ta hanyar riko da gaskiya da tsantsaini wajen tafiyar da ayyukan hukumar gaba daya domin bunkasa ayyuka.
Wani abin lura kuma wanda ya fi daukar hankali da ban sha’awa a cikin sabbin gyare-gyaren shi ne, tunanin sauya ayyukan hukumar su koma sabuwar hanyar gudanarwa, wanda ko shakka babu zai bude wani sabon shafi na fata da kishin kasa a tarihin gudanar da aikin hajji a Najeriya.
Shugaban hukumar ta NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana shirinsa da kuma kudirinsa na daga darajar hukumar zuwa wani mataki babba ta hanyar yin amfani da hanyar zamani da kuma horas da ma’aikatan hukumar.
Farfesa Saleh, ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin aikin hajjin Hausa, “Hajji Kiran Allah” wanda NAHCON ke shiryawa.
Wani bangare na fa’idar sauya tsarin ayyukan hukumar ta sabuwar hanyar da duniya ke tafiya a yanzu, a cewar Farfesa Saleh Pakistan, za a samarwa mahajjata wata na’urar hannu yayin da suke kasa mai tsarki, wanda zai taimaka da kuma saukaka gano alhazan da suka bata idan aka yi la’akari da ci gaban abubuwan inganta rayuwa da ke faruwa a kasar Saudiyya, ko da irin wadannan alhazai ba sa jin harshen Larabci ba.
Wata muhimmiyar fa’ida sauya yadda ayyukan hukumar ke gudana ta sabuwar hanyar zamani ta duniya a cewar Farfesa Abdullahi Pakistan, shi ne, sauƙin adanawa, samun dama da kuma duba bayanai game da ayyukan hukumar a ko’ina, kowane lokaci a duk faɗin duniya.
Tabbas wannan wani babban hangen nesa ne wanda shugabancin hukumar alhazai ta kasa, karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Pakistan.