Gwamnatin Jihar Legas ta kafa wani kwamitin wucin gadi domin shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya.
A sanarwar da Daraktan Hulda da jama’a na Hukumar, Taofeek Lawal ya fitar, yace an ƙaddamar da kwamitin, wanda Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci, Dr. Ahmad Abdullahi Jebe ke jagoranta ne ta hannun Kwamishinan Harkokin Gida, Olanrewaju Ibrahim Layode, a sakatariyar gwamnati da ke Alausa, Ikeja, a ranar Laraba.
Da yake jawabi ga mambobin kwamitin, Layode ya bayyana cewa an naɗa su ne bisa la’akari da ƙwarewarsu da jajircewarsu, domin tabbatar da ingantaccen tsari, daidaitawa da kuma gudanar da ayyukan da suka shafi Hajjin 2026 cikin nasara.
Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu da cikakken ƙwazo, gaskiya da riƙon amana, bisa manufofin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmi ta Jihar Legas.
A cewarsa, aikin kwamitin ya haɗa da bayar da gudummawa a fannoni kamar daidaita harkokin sufuri da kayan aiki, kula da jin daɗin maniyyata, masauki, shirye-shiryen lafiya, da sauran ayyukan da za a iya ɗora musu lokaci zuwa lokaci.
Yayin da yake taya su murna, ya jaddada cewa naɗin nasu ya fara aiki nan take kuma zai ci gaba har zuwa ƙarshen aikin Hajjin 2026.
Da yake mayar da jawabi a madadin sauran mambobi, shugaban kwamitin, Dr. Ahmad Jebe, ya gode wa Gwamna, Babajide Olusola Sanwo-Olu; Mataimakin Gwamna, Kadiri Obafemi Hamzat; da kuma Kwamishinan Harkokin Gida, bisa ba su wannan dama ta yi wa jihar hidima.
Ya tabbatar da cewa za su mutunta amanar da aka ɗora musu, tare da alƙawarin yin aiki tukuru domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin. Haka kuma ya roƙi a ba su cikakken goyon baya domin sauƙaƙa aikin da ke gabansu.
Daga nan ya sanar da rabon ƙananan kwamitoci da shugabanninsu kamar haka: Masauki (Hon. Musliudeen Maiyegun); Jin Daɗi (Malam Ajisegiri Ismail Ajibade); Manifet, Biza da Yaɗa Labarai (Hon. Waheed Lolade Shonibare); Madina/Mina da Arafat (Engr. Shakiru Ayinde Gafar).
Sauran sun haɗa da Wa’azi/Wayar da Kai (Farfesa Kabir Paramole); Sufuri (Alhaji Mojeed Sanni) da Kwamitin Kayan Jaka da Auna Nauyi (Alhaji Yusuf Ara).
A halin yanzu, Hon. Layode ya bayyana cewa jigilar maniyyata 1,600 na Jihar Legas za ta fara ne a ranar Alhamis, 7 ga Mayu, da jirgi na farko mai ɗauke da maniyyata 345.
A cewarsa, za a ci gaba da jigilar kamar haka: jirgi na biyu ranar Juma’a 8 ga Mayu; na uku ranar Lahadi 10 ga Mayu; na huɗu ranar Talata 12 ga Mayu; yayin da jirgi na ƙarshe zai tashi ranar Laraba 13 ga Mayu, 2026. Ya ce an tsara hakan ne bisa jadawalin da National Hajj Commission of Nigeria ta fitar.
Haka kuma ya sanar da kwamitin cewa kamfanin jirgin sama na Flynas, wanda NAHCON ta zaɓa domin jigilar maniyyatan jihar, ya amince da ƙara nauyin kaya daga kilogiram 32 zuwa 46. Ya ƙara da cewa kowanne maniyyaci zai samu jakunkuna biyu masu nauyin kilogiram 23 kowanne domin manyan kaya, yayin da kayan hannu zai ci gaba da kasancewa kilogiram 8.
