Jirgin farko na aikin Hajjin 2026 daga Najeriya zai tashi daga Filin Jirgin Sama na Gateway International Airport da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, a ranar 3 ga Mayu 2026 tare da kamfanin jirgin sama na FlyNas.
A sanarwar da mataimakiyar Daraktar yada labarai da dab’i ta Hukumar, Fatima Sanda Usara, wannan ne karon farko da maniyyatan Jihar Ogun za su tashi daga cikin jihar, sakamakon kammala gina filin jirgin.
Haka kuma, a wannan rana ce jiragen Umza da Max Air za su tashi daga Abuja dauke da maniyyatan jihohin Kogi da Nasarawa, yayin da Air Peace zai tashi daga Legas dauke da maniyyatan Jihar Oyo. Sannan wani jirgin FlyNas zai tashi daga Birnin Kebbi.
A sakamakon haka, ma’aikatan NAHCON, ciki har da na wucin gadi daga cikin Tawagar Likitocin Kasa, sun riga sun tashi a yau Talata 28 ga Afrilu domin yin shiri kafin isowar maniyyatan Najeriya.
Hukumar NAHCON ta shawarci maniyyata da su lura cewa jigilar su ta jiragen sama za ta gudana ne yanki bayan yanki. Da zarar an kammala jigila daga wani yanki aka wuce na gaba, kamfanin jirgin ba zai sake dawowa wannan yankin ba.
Duk wanda ya rasa jirginsa daga yankin da aka tsara masa, zai fuskanci sakamakon komawa jiran wani sabon tsari a gaba.
Haka zalika, an sanar da cewa dole ne maniyyata su yi tafiya karkashin rukuni na mutane 45, inda katin Nusuk dinsu zai kasance a shirye yana jiran isowarsu a Saudiyya. Saboda haka, ana shawartar kowane maniyyaci ya tabbatar da sanin ‘yan rukuninsa kafin tafiya.
Haka nan, ana bukatar maniyyata su samu lambobin waya na shugabannin rukuninsu da kuma jami’an jiha da za su raka su a jirgin.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar wa da maniyyatan Najeriya cewa Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin ganin an gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara da kwanciyar hankali.
