Kalubalen aiki sun kusan durƙusar da harkokin Filin Jirgin Sama na King Khalid da ke Riyadh, inda dubban fasinjoji da ke tafiya zuwa da daga filin jirgin suka makale sakamakon soke jirage da jinkiri da yawa, yayin da manyan kamfanonin jiragen sama suka kasa samar da madadin jirage cikin gaggawa.
Kamfanonin jiragen sama na Saudia da flyadeal na daga cikin wadanda suka fuskanci matsalolin, inda suka fitar da sanarwa suna danganta lamarin da kalubalen aiki na wucin gadi.
A wata sanarwa da filin jirgin sama ya wallafa a shafinsa na X, an bukaci matafiya da su tuntubi kamfanonin jiragen sama kai tsaye kafin su nufi filin jirgin, domin tantance sabbin bayanai da lokutan tashin jiragensu.
Sanarwar ta ce:
“Filin Jirgin Sama na King Khalid yana sanar da ku cewa, sakamakon haduwar wasu dalilai na aiki a cikin kwanaki biyu da suka gabata ciki har da karkatar da wasu jirage daga wasu filayen jirgin sama zuwa King Khalid, tare da ayyukan gyara da aka tsara a tsarin samar da man fetur hakan ya yi tasiri ga jadawalin wasu jirage, ciki har da jinkiri ko soke wasu jiragen da wasu kamfanonin jiragen sama ke gudanarwa.”
Filin jirgin ya kara da cewa kungiyoyin aiki na kokarin gyara lamarin ba dare ba rana, tare da hadin gwiwa da kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki, domin dawo da daidaiton ayyuka cikin gaggawa, tare da daukar dukkan matakan da suka dace don rage duk wani tasiri ga karuwar fasinjoji.
Majiyoyi a filin jirgin sun shaida wa majiyarmu cewa matsalar na da alaka da ruwan sama mai yawa da aka samu a Riyadh a ranar Juma’a. Rahotanni sun nuna cewa ruwa ya shiga cikin tankokin man fetur da ake amfani da su wajen cika jirage kafin tashi, lamarin da ya janyo wahalar sake tsara tafiye-tafiyen fasinjoji ga wasu kamfanonin jiragen sama.
A anarwar da ta wallafa a X, Saudia ta ce:
“An riga an fara tuntubar baki (fasinjoji) da abin ya shafa ta hanyoyi daban-daban na sadarwa, kuma ana aiwatar da dukkan canje-canjen tikiti ba tare da karin kudi ba.”
Majiyarmu ta tuntubi Saudia domin karin bayani.
Haka zalika, a wani sako da ta wallafa a X, flyadeal ta ce dukkan fasinjojinta da rikicin ya shafa “za a sanar da su kai tsaye ta imel da sakonnin SMS, tare da ba su zabin sake yin rajista da tallafin da ya dace.”
(Arab News)
