Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince da biyan kuɗin da ya yi ragowa ga mahajjata ɗari da tara (109) waɗanda suka fara ajiya da ₦8,500,000 da kuma ₦8,440,000 domin aikin Hajjin shekarar 2026.

A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a yau yayin wata hira da ‘yan jarida a ofishinsa.

Ya bayyana cewa mahajjata dari biyar da casa’in da uku (593) ne suka biya kuɗin ajiya tun kafin sanar da cikakken kuɗin Hajji.

Saboda haka, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya yi kira ga sauran mahajjatan da abin ya shafa da su garzaya zuwa Hukumar domin karɓar kuɗin da ya rage musu kafin a fara jigilar maniyyata ta na wannan Shekara.

Da yake jawabi kan batun wadanda suka Biya kudin Aikin Hajji na Bana ta hukumar,  Darakta Janar ɗin ya ce mahajjata dubu uku da dari shida da bakwai (3,607) ne suka Biya ta hukumar  izuwa yanzu domin aikin Hajjin 2026.

Ya kuma ƙara da cewa Hukumar ta riga ta biya fiye da naira biliyan 23 ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a madadin waɗannan maniyyata da suka Biya kudaden su.

Darakta Janar ɗin ya kuma yi kira ga mahajjatan da har yanzu ba su miƙa fasfo ɗinsu na fita kasar waje ba wato (International Passport)  da su gaggauta yin hakan domin sauƙaƙa aikin fitar da biza.

Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano  bisa goyon baya da gudummawar da take bayarwa domin jin daɗin mahajjatan jihar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version