Majalisar kasa a yau 10 ga watan Oktoba 2024, ta tabbatar da nadin Farfesa Saleh Abdullahi Usman a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

 

Ya karbi mukamin shugaba na 6 bayan Malam Jalal Ahmed Arabi bayan sauyin shugabancin hukumar. 

 

A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da Jama’a ta Hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace, tabbatar da hakan na zuwa ne bayan kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje ya tantance Farfesa Usman a ranar 8 ga Oktoba 2024.

 

Tabbatar da hakan ya nuna amincewar Majalisar ga sabon Shugaban Hukumar NAHCON ta hanyar gudanar da ayyukanta na tabbatar da aikin Hajji mai inganci da nasara ga Alhazan Najeriya.

 

Farfesa Sale Abdullahi ya nuna jin dadinsa kan amanar da bangarorin gwamnati da na majalisar dokoki suka ba shi.

 

Ya yi alkawarin dorawa kan nasarorin da Shugabanmin da suka gabace shi suka samu wajen tabbatar da ci gaban aikin Hajji a Najeriya, tare da mai da hankali kan jin dadin alhazan Najeriya da yadda za su iya gudanar da aikin Hajji mabrur (Hajji karbabbe).

 

Bayan Da majalissar dokokin kasar ta tabbatar da Farfesa Usman, ya ba da tabbacin ci gaba da jajircewa wajen ganin hukumar NAHCON ta bunkasa da kuma neman addu’a da goyon bayan kowa wajen cimma burin masu ruwa da tsaki.

 

“Za mu ci gaba da inganta ayyukanmu ga mahajjatan Najeriya, tare da yin aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki don samar da aikin hajji mai cike da aminci.”

 

Shugaban ya taba yin aikin a karkashin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano a matsayin Shugaban Hukumar.

 

Canjin shugabancin ya zo ne a daidai lokacin da hukumar NAHCON ke shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a daidai lokacin da Saudiyya ta kayyade.

 

Ana sa ran tabbatar da Shugabancin zai hanzarta shirye-shiryen. Ana kuma sa ran za a kara inganta hadin gwiwar Hukumar da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin Hajji ga dukkan maniyyatan Najeriya.

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version