Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Jihar Kogi ta nuna cikakken goyon bayanta ga sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, inda ta bayyana nadin nasa a matsayin wanda ya samo asali daga cancanta da kuma kima.

 

A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar Yada labarai da Dab’i ta Hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace an bayyana wannan goyon baya ne a yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Sheikh Salman Adam Imam, ta kai hedikwatar NAHCON da ke Abuja, inda suka taya sabon shugaban murna tare da yi masa addu’ar samun nasara a jagorancinsa.

 

A cikin wata sanarwa da aka gabatar yayin ziyarar, majalisar ta bayyana cewa nadin Yusuf ya samo tushe ne daga “kyakkyawan tarihin aikinsa, ƙwarewar gudanarwa da aka gwada, da kuma gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ɗabi’u nagari,” tana mai ƙara da cewa irin wannan tarihin zai ba shi damar jagorantar hukumar a wannan muhimmin lokaci.

 

Malaman addinin sun kuma jaddada muhimmancin wannan nadin, inda suka nuna cewa Yusuf shi ne ɗan asalin Jihar Kogi na farko haka kuma daga yankin Arewa ta Tsakiya da ya zama shugaban hukumar tun bayan kafuwarta kusan shekaru talatin da suka gabata.

 

Sun bayyana nadin a matsayin abin alfahari ga kowa, tare da taya al’ummar Musulmi ta ƙasa baki ɗaya murna, musamman mutanen Jihar Kogi da yankin Arewa ta Tsakiya.

 

Majalisar ta kuma gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa abin da ta kira “kyakkyawan zaɓi mai hikima,” tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewa da shugabanci na sabon shugaban za su taimaka wajen sake farfaɗo da NAHCON da kuma dawo da amincewar jama’a ga hukumar.

 

Ta kuma yi kira ga shugabanni da ma’aikatan hukumar, da kuma duk masu ruwa da tsaki a cikin al’ummar Musulmi, da su bai wa Yusuf cikakken goyon baya domin tinkarar ƙalubalen da ke akwai da kuma inganta ayyukan hukumar.

 

An kuma miƙa masa takardar taya murna a hukumance yayin ziyarar.

 

Da yake mayar da jawabin, Ambasada Yusuf ya nuna godiyarsa bisa wannan goyon baya, yana mai cewa ziyarar ta ƙara masa ƙwarin gwiwa. Ya yi alƙawarin cika amanar da aka ɗora masa, yana mai tabbatar da cewa jagorancinsa zai yi ƙoƙarin wuce abin da ake tsammani tare da kawo ci gaba mai ma’ana a ayyukan hukumar.

 

A ƙarshe, an yi addu’o’i domin samun nasara a jagorancinsa da kuma ci gaban hukumar gaba ɗaya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version