Hukumar aikin ta Najeriya (NAHCON) ta  sanar da nadin Dr. Mustapha Muhammad Ali a matsayin sabon sakatare na hukumar. 

Hukumar NAHCON ta fara gagarumin shirin aikin Hajin 2025

Nadin nasa ya biyo bayan samun amincewar majalisar gudanarwar Hukumar ta biyar yayin taronta a ranar 26 ga Fabrairu 2025 daidai da tanadin sashe na kashi 8 na Dokar da ta Kafa NAHCON (2006).

 

Dr. Mustapha Muhammad Ali zai yi aiki a matsayin sakatare na tsawon shekaru hudu (4) a zangon farko, inda wa’adin nasa zai fara daga ranar da ya kama aiki. Matsayinsa zai zama mai fasaha wajen tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa da kuma aiwatar da manufofi da samar da ingantaccen aiki da tasirin ayyukan hajji a Najeriya.

 

Dr Ali wanda ya kasance gogaggen Jami’in gudanarwa, tsohon Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Borno kuma jajirceccen jami’i mai kwarewa a fannin gudanar da harkokin aikin Haji kuma kasancewarsa hakan zai taimakawa Hukumar ta NAHCON wajen bunkasa harkokin kula da Maniyyata

 

NANCON ta Bayyana kwarin Gwiwarta kan yadda take ganin cewa Dr Mustapha zai sake fito da kima da darajar ayyukan Hukumar tare da bayar da gudummawarsa wajen bunkasa harkokin ayyukan Haji

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version