Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da samun rangwamen kudi fiye da naira biliyan 19 domin aikin Hajjin shekarar 2026, bayan tattaunawa da masu samar da ayyuka a Saudiyya.
Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Kano, jim kadan bayan dawowarsa daga ziyarar aiki da ya kai Kasar Saudiyya.
Ya bayyana cewa rangwamen ya kawo saukin fiye da naira dubu 200 ga kowanne mai niyyar tafiya, wanda shi ne ya sa aka samu raguwar kudin aikin Hajji da aka sanar a baya. Najeriya ta samu kujeru 66,910 domin Hajjin bana.
A bisa farashin da aka amince da shi, alhazai daga Maiduguri da Yola za su biya naira 8,118,333.67, daga jihohin Arewa kuma naira 8,244,813.67, yayin da alhazai daga Kudu za su biya naira 8,561,013.67.
NAHCON ta rattaba hannu kan kwangila da Kamfanin Mashariq Dhahabiyya domin hidimomi a Mashā’ir da kuma Kamfanin Daleel Al-Ma’aleem domin sufuri. Farfesa Saleh ya ce: “Mun dawo da godiya ga Allah Madaukakin Sarki tare da sabuwar aniyar aiki. Lokacin da na tafi ranar 22 ga Satumba, manufata ɗaya ce: kare alhazai ’yan Najeriya, tabbatar da ayyuka masu inganci a farashi mai sauki, da kuma shirya filin gudanar da hajjin 2026 cikin nasara.”
Haka kuma, ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen masauki da abinci a Madina, inda aka samu ingantattun wuraren zama a yankin Markaziyya a farashi mai sauƙi.
Shugaban NAHCON ya kuma sanar da cewa duk mai niyyar tafiya dole ne ya biya aƙalla kashi 50 cikin 100 na kuɗin aikin Hajji kafin 8 ga Oktoba, 2025, sannan ya cika ragowar kuɗin gaba ɗaya kafin 31 ga Disamba, 2025.
Ya ce an sanya wannan wa’adin ne domin biyan sharuddan Saudiyya da kuma tabbatar da wuri wajen tantuna da ingantaccen aiki ga maniyyata.