Yayin da watan Ramadan ya kama, a madadin Mambobin Hukumar da Gudanarwa da daukacin ma’aikatan Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh na mika sakon taya murna da fatan alheri ga daukacin al’ummar Musulmi a fadin kasar nan.
Wannan wata mai alfarma lokaci ne na zurfafa tunani na ruhi, tarbiyyar kai, da sabonta ibada ga Allah SWT. Lokaci ne da kofofin rahama da gafara suke budewa, kuma ake yawaita samun ladan ayyukan alheri. Ramadan ba lokaci ne na azumi da addu’a kadai ba amma dama ce a gare mu don karfafa dankon zumunci da ‘yan uwantaka, mu tausaya wa marasa galihu, da neman tsarin Allah a cikin dukkan al’amuranmu.
Shugaban yace Musulmi ya kamata su yi amfani da wannan wata wajen tsarkake zukatansu, sabunta niyya, da himma wajen kyautata ibada da ayyukansu na yau da kullum.
A Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), shugabancinta ya jajirce wajen yi wa al’ummar Musulmi hidima da kuma tabbatar da sun biya bukatunsu na gudanar da aikin Hajji mai alfarma.
A bisa haka ne aka ba da wani lokaci na alheri don ba wa maniyyata damar yin rajista da biyan kudaden shiga aikin Hajjin 2025.
A cewar Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Muna addu’ar Allah SWT ya ba mu ƙarfi da basira don sauke nauyin da ke wuyanmu na ci gaban al’ummarmu. Ina yi mana wasiyya da mu kawar da kanmu daga munanan abubuwa da ka iya hana ci gabanmu a matsayinmu na al’umma, mu yi azumi da ikhlasi, muna neman karin albarka ga al’ummarmu da shugabanninta.
Mu kuma yi addu’ar samun nasarar ayyukan Hajjin bana da kuma lafiya da lafiya ga dukkan alhazai. Allah (SWT) Ya sa mu dace, Ya ba mu ikon yawaita alkhairan da ke cikin wannan wata mai alfarma. Ramadan Mubarak!