Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jahar Sokoto ta sanar da cewa rukuni na farko na alhazan jahar za su tashi zuwa aikin Hajjin shekarar 2026 a ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2026.

A cewar Shugaban sashen yada Labarai da sadarwa na Hukumar Faruku Umar, yace Babban Sakatare na Hukumar, Alhaji Ibrahim Umar JJ, ne ya bayyana hakan a yau yayin wata tattaunawa ta wayar tarho kai tsaye a shirin Sakkatawa Kwallahiya da ake gabatarwa a gidan rediyon Vision FM.

Alhaji Ibrahim Umar JJ ya tabbatar da cewa Hukumar ta samu nasarar kammala dukkanin biza ga alhazai 2,404 daga Jihar Sokoto.

Ya kuma ƙara da cewa dukkan alhazan sun kammala gwaje-gwajen lafiya na wajibi kamar yadda Masarautar Saudiyya ta tanada.

Dangane da batun masauki, Babban Sakataren ya bayyana cewa an samar da ingantattun wuraren zama ga alhazan a yankin Masfala, wanda ke kusa da Harami a Makkah, domin tabbatar da jin daɗinsu da sauƙin gudanar da ibada.

Hukumar ta sake bai wa alhazai da iyalansu tabbacin kudurinta na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version