Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kaddamar da Tawagar Nusuk Masar ta Hajjin 2026 a ofishin Hukumar da ke Makkah.
A sanarwar da Mai taimakawa Shugaban kan harkokin yada labarai, Ahmed Mu’azu ya sanyawa hannu, yace tawagar mai mutane goma za ta jagoranci dukkan mu’amalar Najeriya da Ma’aikatar Haji Da bangaren ragistar Umrah ta Saudiyya, wato Nusuk Masar.
Wannan dandali ne da ke sarrafa muhimman ayyuka na Hajjin 2026, ciki har da yin rijistar mahajjata, fitar da biza, masauki, abinci, kwangilolin ayyukan Mashā’ir da kuma bayanan jiragen sama.
Farfesa Usman ya bayyana cewa aikin da aka dorawa tawagar na da muhimmanci matuƙa wajen shirin Najeriya na gudanar da Hajjin bana.
Ya ce ‘yan Najeriya na sa ran tsarin da zai ba su sahihan bayanai da kuma hidima cikin lokaci. Ya umurci wakilan tawagar da su tabbatar da bin ka’ida a dukkan ayyukan da aka basu.
Ya jaddada cewa jin daɗin kowane ɗan Najeriya da zai je Hajji zai dogara ne da yadda tsarin da suke kula da shi zai yi aiki. Ya ce yadda za a yi aiki a dandalin Nusuk Masar na da daraja kamar yadda ake kallon kamfanonin aikin jiragen sama da sauran masu ba da hidima.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kudi na Hukumar, Prince Aliyu Abdulrazaq, ya bukaci tawagar da ta gudanar da wannan aiki cikin gaskiya da riƙon amana. Ya ce dole su nuna amincewar da aka basu a dukkan matakan gudanar da aiki.
Da yake mayar da jawabi a madadin tawagar, jagoran tawagar, Dr. Haruna Danbaba, ya tabbatar wa Hukumar cewa za su cika dukkan wa’adin da Masarautar Saudiyya ta gindaya. Ya ce wa’adin lokutan da aka kayyade ba su da damar ɓata lokaci ko sakaci.
Wannan kaddamarwa na nuna muhimmiyar nasara a matakan farko na shirye-shiryen aiwatar da shirin Hajjin sun fara nan take.
