Daga Shafi’i Sani Mohammed Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ƙara ɗaukar matakai na musamman domin shirya Hajjin 2026 tare da cikakken goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, domin samar da farashi mai rahusa, sauƙin tafiya, da kuma ibada mai armashi ga alhazai ‘yan Najeriya.

A karkashin jagorancin Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwarta,  Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Hukumar ta fara aiwatar da tsare-tsaren inganta ayyuka, haɓaka hidima, da rage kuɗaɗen da alhazai ke biya.

Dangane da umarnin Shugaba Tinubu na sauƙaƙa kudin aikin Hajji, NAHCON ta sanar da muhimmiyar ragi a farashin Hajj na shekarar 2026.

Sabbin farashin sune:
• ₦7,579,020.96 – Shiyyar Borno/Adamawa
• ₦7,696,769.76 – Shiyyar Arewa
• ₦7,991,141.76 – Shiyyar Kudu

Wannan raguwar tana tsakanin ₦748,000 zuwa ₦793,000 idan aka kwatanta da farashin bara kuma Farfesa Usman ya bayyana hakan a matsayin “shaida ta nuna damuwar gwamnati ga alhazai na Najeriya.”

Ya yabawa Shugaba Tinubu bisa wannan umarni na tausayi da kuma Mataimakinsa Shettima bisa kulawa ta kusa da yake yi wa ayyukan Hukumar, yana mai cewa goyon bayansu ya ƙara kwarin gwiwa wajen ci gaba da sauye-sauyen da ake aiwatarwa.

Domin bai wa mutane damar shiri da wuri, Hukumar ta sanya 5 ga Disamba, 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a karɓi kuɗin alhazai, tare da kira ga masu niyyar tafiya su biya da wuri domin samun sauƙin aiwatar da biza da sauran shirye-shirye.

A wani bangare na shirye-shiryen farkon shekara, tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Usman ta halarci Hajj and Umrah Expo da aka gudanar a ranar 9 ga Nuwamba 2025 a Jeddah, Saudiyya.

Taron ya tara manyan masu ruwa da tsaki na Duniya kan harkokin Hajj da Umrah, inda ya kasance dama ga NAHCON wajen ƙarfafa alaƙa da gano sababbin hanyoyin gudanar da ibada.

Tun da farko, Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ta Hajj da Umrah ta shekara ta 2026 tare da Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya wanda ya tabbatar da halartar ƙasar gaba ɗaya a aikin Hajjin badi.

Farfesa Usman ya bayyana rattaba hannun a matsayin “muhimmin mataki da ke buɗe ƙofa ga tsarin gudanar da Hajj cikin gaskiya, bin doka, da ingantaccen tsari.”

A halin yanzu kuwa, tawagar NAHCON da ke Saudiyya ta kammala duba otal-otal da wuraren girki a Madina domin tabbatar da tsafta, tsaro, da jin daɗin alhazai.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan Sashen Tsare-Tsare, Bincike, Kididdiga, Bayar da Bayanai da Laburare (PRSILS), ta duba otal-otal sama da 20 da kuma wuraren girki 7 a yankin Markaziyya.

Irin wannan aikin na ci gaba a Makka inda Kwamishinoni, Mambobin Hukumar, Wakilan Jihohi da Jami’an Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ke gudanar da bincike.

A gida kuma, NAHCON na ci gaba da horar da ma’aikatansa ta hanyar gudanar da laccar bayar da horo ta wata-wata inda zaman baya-bayan nan ya mayar da hankali kan “Rawar da National Reception Team ke takawa wajen nasarar aikin Hajji.”

Farfesa Usman ya jaddada cewa waɗannan shiri da sauye-sauye da haɗin gwiwar da ake yi da hukumomin Saudiyya, na nuna cewa Najeriya ta shirya sosai domin gudanar da aikin Hajji 2026 cikin tsari da kwanciyar hankali.

“Jin daɗi, tsaro, da walwalar alhazai na Najeriya sune muhimman abubuwan da muke mayar da hankali,” in ji shi.

Da wannan tallafi daga gwamnati da shirye-shiryen da aka fara tuni, NAHCON na gina sabuwar kafa ta inganci, gaskiya, da tabbatar da walwalar alhazai domin aikin Hajj 2026 mai cike da nasara

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version