Daga Ibrahim Abubakar Nagarta

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bar Legas zuwa jihar Kebbi a yau, 19 ga Disamba, 2025 tare da tawagarsa, a ci gaba da ziyarar Fahimtar juna a wasu muhimman shiyyoyin gudanar da aikin hajji a fadin Najeriya.

 

A yayin da Hukumar ta NAHCON a jihar Legas karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh ta ziyarci mataimakin gwamnan jihar Dr. Hamzat da Oba na Legas mai martaba Rilwan Babatunde Akiolu da kuma kungiyar kamfanoni masu jigilar Hajji da Umrah ta jihar Legas, inda shugaban NAHCON ya kaddamar da sabon ofishin kungiyar

Idan dai za a iya tunawa, Farfesa Abdullahi Saleh da tawagarsa ta gudanar da ziyarar ne a Maiduguri a makon da ya gabata a matsayin wurin da suka fara ziyarce-ziyarce a shiyyar.

 

Shugaban NAHCON a lokacin da ya je Maiduguri, ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba El-kanemi na Borno Abubakar ibn Umar Garbai da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum.

 

A jawabinsa yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya yi alkawarin bayar da duk wani taimako da ya dace wajen inganta da kuma bunkasa aikin Hajji a kasar nan.

 

A yayin da ya je jihar Kebbi, ana sa ran shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Usman, zai gana da manyan jami’an gwamnati da malaman addini da masu ruwa da tsaki a harkokin aikin hajji, duk a kokarin da ake na ganin an cimma nasarar da ake bukata a aikin hajjin 2025.

 

Ibrahim Abubakar Nagarta

Kodineta na kasa, Tawagar Taimakon Yada Labarai Ta Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version