Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan a yau yayin wata ziyara da ya kai cibiyoyin karatun koyon Aikin Hajj na kananan hukumomin Ungogo da Bichi, a wani bangare na shirin Hajjin shekarar 2025.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: 2025 Hajj: Hukumar Alhazai ta Kano ta fara raba Jakar hannu da Uniform ga Maniyyata
A cikin sanarwar da Jami’in Hulda Da Jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa, bisa ga jadawalin da Hukumar kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, cewa Jihar Kano za ta fara jigilar alhazanta zuwa Saudiyya tare da kamfanin jirgin sama na Max Air a ranar 13 ga Mayu, 2025.
Ya kara da cewa Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata tun da wuri, domin tabbatar da cewa an gudanar da jigilar alhazan cikin nasara da tsari.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya ja hankalin mahajjata masu niyyar tafiya da su rika halartar karatun koyon Aikin Hajji a kai a kai domin amfanin kansu.
Haka kuma, ya gargade su da su kiyaye bin dokoki da ka’idojin na hukumomin Najeriya dana wadanda Saudiyya suka shimfiɗa domin tafiyar da aikin Hajji.
Shugaban Hukumar tare da dukkan mambobin kwamitin da daraktoci sun halarci wannan ziyarar.